Shin ƴan hamayya za su iya dunƙulewa kafin 2027?

Peter Obi da Atiku da Rabi'u Musa Kwankwaso

Asalin hoton, BBC/Collage

Lokacin karatu: Minti 4

Abubuwan da suka faru a baya-bayan nan tsakanin jam'iyyun hamayya inda suke nuna walle-walle da juna na jefa shakku a zukatan masu nazarin kimiyyar siyasa dangane da yiwuwar dunƙulewar su wuri guda wajen ƙalubalantar jam'iyya mai mulki a 2027.

A makon da ya gabata ne wasu ƴan majalisar dattawa da wakilai har guda bakwai suka fice daga jam'iyyunsu na hamayya zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Haka kuma mutumin da ya ya zama mataimaki ga ɗntakar shugabancin Najeriya na jam'iyyar LP a 2023, Sanata Datti Baba-Ahmed wanda ya ce ba zai bi abokin tafiyar tasa zuwa jam'iyyar haɗaka ta ADC ba.

Shi ma Injiniya Buba Galadima wanda jigo ne a tafiyar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP, ya sha faɗin cewa Kwankwaso ba zai je jam'iyyar haɗaka sai dai a zo a same su a jam'iyyar tasu.

Dalilan da suka hana ƴan hamayya haɗewa

Farfesa Tukur Abdulƙadir malami a jami'ar jihar Kaduna, KASU kuma mai nazarin kimiyyar siyasa ya lissafa dalilai guda uku da ya ce ɗaya daga cikinsu ne ka janyo jan ƙafa daga ƴan hamayya.

  • Likimo: Akwai yiwuwar cewa ƴan hamayyar dungu suke yi wa jam'iyya mai mulki domin ka da su bayar da ƙofar da za ta fahimci inda suka dosa. Kila daga baya za su iya haɗewa su manta da bambance-bambance da ke tsakaninsu kamar yadda aka gani a 2015 lokacin da aka kafa jam'iyyar haɗaka ta APC.
  • Burun ƴan siyasa na takara: Akwai yiwuwar cewa son rai da burin da ƴan siyasar suke da shi na tsayawa takara ka iya zama dalilin gaza haɗewar ƴan hamayyar. Misali Atiku Abubakar da alama yana kan bakarsa na son yin takara. Shi ma Peter Obi ya lashi takobin yin takara. Haka ma Rotimi Amaechi ya bayyana burinsa na takara. Shi ma Rabi'u Musa Kwankwaso ana ganin burinsa na takara ne zai iya hana shi dunƙulewa da jam'iyyar hamayya.
  • Hannun jam'iyya mai mulki: Akwai masu hasashen cewa rashin haɗin kan ƴan hamayyar ba zai rasa nasaba da irin rawar da jam'iyyar APC mai mulki za ta iya takawa wajen kunna da kitsa rikice-rikice a tsakanin ƴan hamayyar.

Illar rashin haɗin kai tsakanin ƴan hamayya

Farfesa Tukur Abdulkadir ya ce babbar illar da rashin haɗewar ƴan hamayyar za ta yi shi ne bai wa jam'iyya mai mulki damar sake lashe zaɓe.

"Sakamakon zai iya kasancewa jam'iyya mai mulki za ta ci gaba da mulki tunda ba a samu ƙwaƙƙwarar jam'iyyar adawa da ke da karɓuwa da yawa a ɓangarorin ƙasa ba." In ji Farfesa Tukur

"Bisa tsarin siyasar Najeriya, zai wuya su iya samun nasarar ba tunda ba su da gwamnoni da ƴan majalisa da sauran wakilai. Wataƙila mutane su ce ai an yi irin hakan a 2015 lokacin da APC ta ture jam'iyya mai mulki."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"To amma abin da ya kamata su sani shi ne siyasar yanzu ba irin ta lokacin ba ce. Abubuwan da suka taka muhimmiyar rawa a lokacin su ne tasirin marigayi Muhammad Buhari da goyon bayan da Kudu Maso yamma ta bayar da kuma cewa a lokacin haɗakar tana da jiga-jigai da ma tsairarun gwamnoni masu faɗa a ji a jihohinsu," kamar yadda Farfesa Tukur ya ƙara haske.

Shi ma Dakta Kole Shettima na ƙungiyar MacAthur a Najeriya, kuma mai sharhi kan al'amuran siyasa a ƙasar ya ce jam'iyyun hamayyar sun zama tamkar ƙungiyoyi ne masu gasa a tsakaninsu, maimakon mayar da hankali wajen haɗewar.

''Jam'iyyun yanzu ba kamar na da ba ne, yawanci ƙungiyoyi ne da ake kafawa da nufin samun mulki, kowa ƙwalamarsa ita ce ya zama shugaban ƙasa ko ya riƙe kujera kaza'', in ji mai sharhin siyasar.

Kole Shettima ya ce wannan dalilin da ya sa jam'iyyun suka kasa zama wuri guda domin su yi abin da ya fi wa ƙasa alƙairi domin tunkarar jam'iyya mai mulki a babban zaɓen ƙasar da ke tafe nan da shekara biyu masu zuwa.

''Kowa yana yi ne don raɗin kansa, ba don al'umma ba, inda domin al'umma suke yi ai ba sai mutum ya zama shugaban jam'iyya ko shugaban ƙasa ba ko ya riƙe wani matsayi ba'', in ji shi

Me ya sa ake zargin APC da kitsa rikici tsakanin ƴan hamayya?

"Ganin yadda abubuwa ke faruwa ba za a yi mamaki ba idan an ce jam'iyya mai mulki na da hannu a rikicin. Ko dai ba ita ƙirƙira ba, zai iya zama tana da hannu wajen rura rigingimun domin ganin ba su ƙare ba. Haka ake yi a siyasar Najeriya, inda kowace jam'iyya take ƙoƙarin rushe abokiyar hamayyarta ita kuma ta gina kanta." In ji Farfesa Kamilu Sani Fagge na Jami'ar Bayero ta Kano, wanda ya ce akwai ƙamshin gaskiya a zargin.

Sai dai kuma Farfesa Fagge ya ce dabara ta ragewa jam'iyyun hamayya su gyara gidansu domin ita jam'iyya mai mulki a har kullum tana son ci gaba da mulki ne kuma za ta yi duk iya yinta wajen ganin hakan ya tabbata.

"Abin da yake gabansu shi ne mulki. Kamata ya yi jam'iyyun hamayya su tsara gidansu ta yadda za su ja hankalin masu zaɓe. Ai da ba APC ba ce take mulki, daga baya ne suka yi gyara, suka haɗe da wasu jam'iyyun, sannan suka kayar da PDP.

"Ya kamata su yi la'akari da cewa duk wanda yake kan mulki yana so ya ci gaba, ya rage nasu su san dabarar da za su yi domin ƙwace mulki."