Abubuwa shida kan zaɓen ƙananan hukumomi a Rivers mai cike da taƙaddama

Asalin hoton, Others
A yau Asabar ne ake sa ran za a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi 23 na jihar Rivers da ke yankin Neja Delta kudancin Najeriya.
Hukumar zaɓen jihar ce ta saka cewa za a gudanar da zaɓen duk da taƙaddamar da zaɓen yake cike da ita.
Masu nazarin kimiyyar siyasa dai na yi wa zaɓen kallon wani gwajin ƴar ƙashi tsakanin gwamna mai ci Fubara Siminalayi da tsohon ubangidansa, tsohon gwamnan jihar, kuma ministan Abuja na yanzu, Nyesom Wike.
Dangane da abubuwan da suka faru BBC ta zaƙulo wasu abubuwa da ya kamata a sani kan wannan zaɓen mai cike da taƙaddama.
1) Takara ce tsakanin Fubara da Wike
Tun a shekarar 2023 ce shugabannin biyu suke takun-saƙa a kan jan ragamar jihar, lamarin da ya sa siyasar jihar ta ɗauki zafi, har ta zama abar kallo da magana a faɗin ƙasar.
Tuni ɓangaren Wike suka ce ba za a yi zaɓen ba, su kuma ɓangaren gwamna Fubara suka ce babu gudu, ba ja da baya sai an yi.
Tun a farko-farkon mulkin Fubara aka fara rikici a game da shugabannin ƙananan hukumomi, inda bayan wa’adin waɗanda Fubara ya gada daga Wike ya ƙare, ya buƙaci su tafi, su kuma suka ce allambaran suna da sauran lokaci.
Ana cikin wannan ne sai Fubara ya sanar da naɗa shugabannin riƙon ƙwarya domin su maye gurbin waɗancan, lamarin da ya tayar da hankali a jihar.
2) Fubara na PDP amma ƴantakarsa na APP
Tun bayan da uwar jam'iyyar PDP ta miƙa wa Nyesom Wike ragamar jagorancin jam'iyyar PDP a jihar Rivers, wasu daga cikin ƴan jam’iyyar PDP, ciki har da waɗanda gwamna Fubara ya naɗa shugabannin riƙon ƙwarya a ƙananan hukumomin jihar bayan wa’adin mutanen Wike ya ƙare sun koma jam’iyyar APP.
Komawarsu APP ke da wuya suka samu tikitin takarar shugabancin ƙananan hukumomi a zaɓen wanda za a yi a yau Asabar.
Hakan ya sa ake tunanin wataƙila gwamna Fubara ne ya tura su can, kasancewar PDP ba a hannunsa take ba.
3) PDP da APC sun ce ba za su shiga zaɓen ba

Asalin hoton, Baruku Felix/Facebook
Jam'iyyar PDP wadda shugabanninta na jihar ke tare da Wike sun dage kai da fata cewa ba za a yi zaɓen ba kuma ba za su shiga ba.
Sanannen abu ne dai a siyasar Najeriya cewa a lokuta da dama, jam'iyyar da gwamna yake so, ita ce ke yin cinye-du a zaɓen ƙananan hukumomi.
Hakan ne ya sa jam’iyyar ta PDP mai mulki a jihar ta gudanar da zanga-zangar rashin amincewa da gudanar da zaɓen.
Shi ma Tonu Okocha, shugaban riƙon ƙwarya na tsagin APC da suke tare da Wike ya ce ba za a yi zaɓe ba saboda kotu ta hana hukumar INEC da jami’an tsaro shiga zaɓen.
A nasa ɓangaren kuma, gwamna Fubara ya ce babu gudu ba ja da baya, inda ya ce ai Kotun Ƙoli ta yi hukuncin cewa dole kowace jiha a Najeriya ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi.
4) Hukunce-hukunce biyu kan zaɓen
A ranar 6 ga Satumba, Mai shari’a I.P.C Igwe na babbar kotun jihar Rivers ya ba hukumar zaɓe RSIEC umarnin ta gudanar da zaɓen, sannan ya buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki a zaɓen su bayar da goyon baya domin tabbatar da zaɓen ya tafi da kyau.
Sai dai a wani hukunci daban da mai shari’a Peter Lifu na babbar kotun tarayya ya yanke a ranar Litinin da ta gabata wato 30 ga Satumba ya buƙaci Sufeto Janar na ƴansanda da hukumar tsaron SSS da su umarci jami'ansu su ƙaurace wa zaɓen bayan lauyoyin APC, ƙarƙashin Joseph Daudu SAN sun buƙaci hakan.
5) Ƴansanda sun ce ba za a yi zaɓen ba
'Yansandan dai sun ce suna biyayya ga umarnin kotun tarayya da ke Abuja da ta hana gudanar da zaɓen, yayin da shi kuwa Gwamna Fubara ya kafe cewa sai an gudanar da zaɓen.
6) Hukumar zaɓen Rivers ta ce ta shirya
A ɓangaren INEC, babban kwamishinan INEC a jihar Rivers, Johnson Alalibo ya ce sun samu oda daga babbar kotun tarayya da ke Abuja da ke hana su bayar da rajistar masu kaɗa zaɓe.
Ya ce RSIEC ta aiko da buƙatar a ba su rajistar, amma kafin su miƙa mata ne kotun tarayyar ta yanke hukunci.











