Kotun ɗaukaka ƙara ta mayar wa Gwamna Sule na Nasarawa nasararsa

Asalin hoton, facebook/AA Sule
Kotun ɗaukaka ƙara da ke zaman ta a Abuja ta yi watsi da hukuncin kotun sauraron ƙorafin zaɓen jihar Nasarawa, inda ta mayar wa Gwamna Abdullahi Sule nasara kamar yadda hukumar INEC ta bayyana a lokacin zaɓen gwamnan jihar na 2023.
A hukuncin da kotun ta yanke yau Alhamis, alƙalan kotun sun bayyana cewa kotun sauraron ƙorafin zaɓen gwamnan jihar Nasarawa ta yi kuskure a hukuncin da ta yanke.
A watan da ya gabata ne dai kotun sauraron ƙorafin zaɓen jihar Nassarawa ta soke nasarar gwamna Abdullahi Sule na jam'iyyar APC, tare da bayyana David Ombugadu na PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen na watan Maris ɗin 2023.
Tun farko, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC, a sakamakon zaɓen gwamnan jihar ta ce Abdullahi Sule na APC ya samu ƙuri'a 347,209, inda ta ce ya doke Ombugadu na PDP, wanda ya samu ƙuri'a 283,016.
Sai dai rashin gamsuwa da hakan ne ya sa jam'iyyar PDP da ɗan takararta suka garzaya kotun sauraron ƙorafin zaɓen gwamna, wanda a ranar 2 ga watan Oktoba ta soke nasarar ta gwamna Sule.
Hakan ne ya sanya APC da lauyoyinta suka ɗaukaka ƙara zuwa kotun ɗauka ƙara da ke Abuja wadda ke zaman yanke hukuncin a yau Alhamsi.
End of Ƙarin labaran da za ku so ku karanta:
Hukuncin kotun sauraron ƙorafin zaɓe

Asalin hoton, facebook/AA Sule, Ombugadu
A hukuncin da ta yanke cikin watan Nuwamba, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan a jihar Nasarawa ta umarci hukumar zaɓen Najeriya (INEC) ta janye takardar shaidar cin zaɓen da ta bai wa Gwamna Abdullahi Sule na jam'iyyar APC.
A wani hukunci da kotun mai alkalai guda uku ta gabatar karkashin jagorancin Mai shari'a Ezekiel Ajayi, mafi rinjayen alƙalan sun ayyana ɗan takarar jam'iyyar PDP, David Umbugadu a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna na 18 ga watan Maris a jihar Nasarawa.
Alƙalan sun gabatar da hukuncin ne ta hanyar manhajar Zoom.














