Yadda na rasa 'yan uwana huɗu a harin Nasarawa

Asalin hoton, .
Kwanaki da suka gabata basu zo wa Idris da iyalansa cikin sauki ba saboda suna cikin mutane da dama da suka rasa 'yan uwansu a harin bam da aka kai ƙauyen Rukubu na jihar Nasarawa wanda ke kan iyaƙa da jihar Binuwai, inda mutum 27 suka mutu.
Harin na jirgi mara matuki na ranar Laraba da ta gabata kamar yadda gwamnan Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya bayyana, hakan ya faru ne yayin da Fulani makiyaya suka shiga jihar Binuwai domin karɓar shanunsu da ke tare da gwamnatin jihar.
Idris ya bayyana raɗaɗin da yake ciki lokacin da yake tattaunawa da BBC, inda ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta biya su diyyar mutane da kuma dabbobinsu da suka rasa a harin.
“Na rasa 'yan uwana guda huɗu a harin kuma abu ne da nake jin raɗaɗinsa idan na tuna da shi, matar ɗan uwana Hassan ta shiga naƙuda sannan ta din ga kuka lokacin da ta ga gawar mijin nata, abu ne da ba zan manta ba."
“Hassan ya bar 'ya'ya takwas da kuma matarsa ɗauke da ciki, inda ta haifi 'ya mace a ranar da rasu, waye zai kula da iyalinsa a yanzu?"
“Wannan ba shi ne karon farko ba da ake kashe mu, mu ba 'yan ta'adda bane ko kuma masu garkuwa da mutane, mu mutane ne da ke ƙoƙarin samun rayuwa mai kyau, muna son gwmanati ta biya mu diyya kuma wannan ya zamanto karo na karshe."
Idris ya bayyana cewa mutane 27 din da aka kashe suna da mata huɗu da kuma yara da yawa, inda ya ce babbar matsalar ita ce ta yanda za su ci gaba da rayuwa.
“Tun kafin a kashe waɗannan mutane, muna kuma wahalhalu a wajen da muke zaune saboda ba a san da zaman mu ba."
“Akwai Fulanin da na sani da suke da shanu kusan 100 a baya, amma yanzu guda 15 kaɗai suke da shi, ba za mu iya ci gaba da zama a haka ba."
Yadda lamarin ya faru

Asalin hoton, .

Asalin hoton, .

Asalin hoton, .

Asalin hoton, .
A tattaunawarsa da BBC, kwamishinan ‘yan sandan jihar Nasarawa Maiyaki Muhammed Baba, wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce sun samu labarin faruwar al'amarin ne da safiyar ranar Laraba.
Ya ce "mun tashi da safen nan aka ce mana an jefa bam, ko kuma wani bam ya tashi, akwai gawarwaki da yawa da shanu waɗanda aka yi asara."
Ya ƙara da cewa yanzu da haka hukumar ƴan sanda na ci gaba da bincike kan lamarin.
Sai dai ya ce ba zai iya cewa komai ba kan ko an jefo bam din ne daga sama ko kuma dasa shi aka yi a ƙasa.
Baba ya ce "Yanzu dai an samu gawa wurin 27, sannan akwai wasu da dama da suka samu raunuka."
Lamarin ya faru ne a wani ƙauye da ke yankin Doma na jihar Nassarawa.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne 'yan sandan Najeriya suka bayyana cewa harin bam ya hallaka mutum 27 da jikkata wasu da dama a ƙauyen Rukubi da ke kan iyaƙar jihohin Nasarawa da Binuwai.
Babu wani martani daga sojojin Najeriya

Asalin hoton, NASARAWA GOVERNMENT
Duk da cewa mutane na ɗaura laifin harin kan sojojin Najeriya, rundunar bata fito ta ce uffan ba kan lamarin har kawo yanzu.
Rahotanni da dama sun bayyana cewa kuskure aka samu, inda jirgin sojojin saman Najeriya ta harba harsasai da nufin cewa 'yan bindiga waɗanda take bibiya.
Ko da a wani taron manema labarai ma a ranar Alhamis din da ta gabata, gwamnan jihar Nasarawa, ya ce yana magana da dukkan jami'an tsaro kan lamarin domin samun gamsassun bayanai.
Gwamnan ya ce ya haɗu da shugabanni da dama daga bangaren fulabi a ƙoƙari da yake na kwantar da hankulan da suka tashi bayan faruwar lamarin.











