Gwamna A. A. Sule: Kammala ayyukan da na fara ta fi muhimmanci sama da wa'adi na biyu

Bayanan bidiyo, A lokacina an zuba jarin dala militan 500 a jihar Nasarawa - A A Sule

Danna hoton da ke sama domin ku kalli bidiyo:

Gwamnan Jihar Nasarawa da ke tsakiyar Najeriya, Abdullahi Alhaji Sule (A.A. Sule), ya ce kammala ayyukan da ya fara ita ce mafiya muhimmanci a gabansa fiye da neman wa’adi na biyu na mulkin jihar.

Gwamna A. A. Sule ya ce ba ya cikin gwamnonin Najeriya da suka damu da sake samun dama karo na biyu don su kammala wasu ayyuka.

A wannan hira ta musamman da abokin aikinmu Yusuf Ibrahim Yakasai, gwamna ya kuma bayyana matsayarsa kan zaben da aka yi wa Sanata Abdullahi Adamu a matsayin shugaban jam’iyyar APC.