Al`ummar jihar Nasarawa na korafi game da tallafin kayan abinci

Rabon tallafi

Asalin hoton, OTHER

A Najeriya, gwamnatocin jihohi na ci gaba da rarraba tallafin kayan abinci ga jama`a don rage masu radadin da suke fuskanta, sakamakon cire tallafin man fetur a kasar.

Jihar Nasarawa ta fara rabon kayan abincin , inda wasu ke korafin abin da aka ba su bai taka kara ya karya ba, yayin da wasu ma ke cewa abin bai kai gare su ba.

.

Asalin hoton, other

Rahotanni sun ce, an raba tallafin kayan abincin ne ga jama`a, a kananan hukumomi 13 na jihar Nasarawar, kayan abincin sun kunshi shinkafa da taliya da kuma man girki.

Wani wanda ya shaida yadda rabon tallafin a garin Keffi ya shaida wa BBC yadda rabon ya kasance.

''Ta hanyar masu unguwanni aka aiwatar da rabon, akwai unguwar da aka raba gwangwani-gwangwani na shinkafa da taliya leda daya wacce aka rabawa mutane biyar, wannan al`amari bai yi wa jama`a dadi ba''.

Wata matar auren mai suna Halimatu ta ce labarin rabon tallafin kawai ta samu, ga shi ita da mai gidanta da yaransu suna cikin mawuyacin hali:

''Abinci idan mun samu yau gobe sai dai mu yi hakuri domin mijina karfinsa ya kare ba ya iya komai, muna rokon gwamnati ta tallafa mana''.

Sai dai yayin da wasu mutanen jihar Nasarawar ke kokawa, Barista Yusuf Musa, babban sakatare a ma`aikatar watsa labarai ta jihar, kuma dan kwamitin raba tallafin na jihar, ya bayar da hakuri, kuma ya ce wannan kaso na farko ne aka raba inda ya shaida wa BBC cewa,''Abin da muka samo daga gwamnatin tarayya zuwa jiha shi ne aka fara rabo, muna bai wa jama`a hakuri kar a raina abin da aka samu a yanzu, da yardar Allah a kaso na biyu mutane za su ga canji a sabon tallafin''.

Ba wai a jihar Nasarawa kadai ba, yanzu haka miliyoyin 'yan Najeriya na nan a jihohi daban-daban, suna dakon irin wannan tallafi da aka alkawarta musu, don samun sassaucin matsin da suke ciki.