Illolin wasan tsoratarwa ga ƙananan yara

प्रतीकात्मक तस्वीर.

Asalin hoton, GETTY IMAGES

    • Marubuci, आदर्श राठौर
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, बीबीसी हिंदी के लिए
  • Lokacin karatu: Minti 7

Wata sara da ta karaɗe shafukan sada zumunta a baya-bayan nan wadda iyaye ke "wasan tsoratarwa" da ƴaƴansu domin suga martaninsu na iya rasa wani muhimmin al'amari - ƙananan yara ba lalle su kasance sun kai matakin da za su kalli wasan a matsayin na tsoratarwa ko ban dariya ba.

Wani wasan zolaya na tashe a shafukan sada zumunta inda iyaye ke fasa ƙwai a kan ƴaƴansu ƙananan.

An wallafa dubban hotunan bidiyo a sassan duniya a manhajar TikTok da Instagram inda aka yi wa wasan taken #eggcrackchallenge a Turancin Ingilishi, wanda miliyoyin mutane suka kalla.

Galibin yaran da aka gani a bidiyon ko dai ƙananan yara ne ko kuma shekarunsu ba su wuce biyar zuwa shida ba.

A waɗannan hotunan bidiyon, ana iya ganin wasu yara sun firgita a lokacin da aka fasa ƙwai a kansu. Wasu kuma na kukan sun ji zafi, wasu suna fara kuka, wasu ma har ta kai ga sun ture iyayensu.

Wannan ya nuna cewa galibin yaran ba sa kallon wasan a matsayin na ban-dariya duk da cewa iyayensu da ke naɗar bidiyon suna dariya a lokacin wasan.

Masu nazari kan halayyar ɗan'aɗam sun ce abu ne da aka yi hasashen zai faru saboda yara ba sa iya fahimtar irin waɗannan wasannin na zolaya ko tsoratarwa.

Mene ne wasan zolaya?

प्रतीकात्मक तस्वीर.

Asalin hoton, GETTY IMAGES

Wani masanin halayyar ɗan'adam Rajesh Pandey ya ce ana yin wasan zolaya ne don saka wani dariya.

Ya ce abin da ke saka farin-ciki da jin daɗi a zukatan mutane shi ake kira abin nishaɗi. Kamar yin wasa da nufin zolaya. A nan, wanda ya yi wasan yana jin daɗin hakan sannan wanda ake yi wa wasan ma haka.

Akwai nishaɗantarwa a wasannin zolaya amma a nan, ana gudanar da wani gwaji kan bil adama. Matsalar ita ce a gwajin, mutumin na iya cutuwa, zai iya tsorata ko ma ya ji ba daɗi.

Da yake bayar da misali, Rajesh Pandey ya ce, "Idan wani ya ja ƙafar yaro da ke shiga aji, ya sa ya faɗi, kowa zai yi dariya. Amma wanda ya faɗin na iya jin rauni. Wannan shi ma wasan zolaya ne amma ana iya kallon shi a matsayin wata hanya ta nishaɗantarwa."

Bambancin wasan zolaya da na tsoratarwa

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mutane na jin babu daɗi idan suka ga ana zolayar yara ƙananan saboda akwai ɗan bambanci tsakanin zolaya da kuma cin zarafin wani. Zolaya na iya zama cin zarafi idan wanda aka yi wa zolayar ba shi da ƙarfi sosai.

Akwai tsarin yin wasan barkwanci - 'saka mutane nishaɗi ba wai cin fuska ba'. Hakan na nufin ana amfani da fitattun mutane don bai wa wasu abin dariya ba wai mutane masu rauni ba. A wajen wasan zolaya kuma, ana yin su ne kan ƙananan yara.

Rachel Melville-Thomas mai magana da yawun ƙungiyar masu nazari kan halayyar ƙananan yara a Birtaniya ce.

Ta ce ana iya kallon wasan zolaya ya yi nasara idan wanda aka yi wa ya fahimci cewa an yi ne domin nishaɗantar da shi, bai ji ƙunci a zuciyarsa ba kuma shi ma ya ɓuge da dariya.

Ta ƙara da cewa, "Muna son mu yi dariya tare. Yin hakan na ƙara kusanto da mutane daban-daban kusa. Wasan zolaya na zama abin nishaɗi idan wanda aka yi wa ɗin nan da nan shi ma abin ya ba shi dariya har ta kai ga ya fahimci an yi ne da nufin zolayarsa. Amma hakan ba ɗaya ba ne da fasa ƙwai a kan wani."

Tasirin hakan a zuciyar ƙananan yara

A wasan tsoratarwa, akwai wanda bai fahimci zolayar sa ake ba. Dariyar da ke zuwa bayan kaɗuwa, ba abu ne mai sauƙi ba ga ƙananan yara su fahimta.

Ga ƙananan yara da ke tasowa, abu ne mai wuya su gane abin dariya nan take. Sai dai, daga shekarun farko na rayuwarsu, yara suke fara gane abubuwan da ke sa su dariya.

Wasu masu bincike sun gano cewa yaro na fara fahimtar abin dariya tun yana shekara biyar zuwa shida. Wasu yaran su kan fara gane wasannin zolaya tun suna shekara huɗu. Suna ci gaba da koyo ne har sai sun fara mallakar hakalinsu.

Wani tsari na abin da ke bai wa mutane dariya shi ne wanda ya bambanta da abin da aka yi tsammani. Wannan ne ya sa mutane ke samun nishaɗi a kallon hotuna masu motsi na yara wato cartoon.

Ko wasan zolaya na sa yara daina yadda da iyayensu?

प्रतीकात्मक तस्वीर.

Asalin hoton, GETTY IMAGES

Melville Thomas ta ce, "Misali, yara kan ishaɗantu idan suka ga hula a kan giwa. Amma matsalar da ke tattare da wasannin zolaya irin na fasa ƙwai a kan yara ita ce sai ka fara samun yardar yara sannan kuma ka razanar da su. Misali, "Mu dafa abinci tare damahaifiya." Sai kwatsam ka fasa masu ƙwai a ka sannan ka sa su ji ba daɗi."

Paige Davis, ita ma masaniya kan halayyar ɗan'adam a Jami'ar York St John da ke Ingila, ta wallafa littafi kan yadda barkwanci ke kasancewa wajen yara.

Ta ce, "a wasan fasa ƙwai a kan yaran, manyan sun san abin da za su yi amma shi yaron bai sani ba. Shi ya sa bai fahimci dalilin da ya sa aka fasa masa ƙwai a ka ba maimakon a cikin kwano. A bidiyo da dama, yaran ba su fahimci cewa zolayarsu a ke ba. Hakan na rage yardarsu ga iyaye."

Masaniyar halayyar ƙananan yara Rachel Melville-Thomas ta bayyana makamanciyar wannan damuwar. Ta ce, "Ga yaron da yake ƙasa da shekara biyar, kai ne garkuwarsa. Ya amince cewa ba za ka taɓa cutar da shi ba. Amma idan ka fasa masa ƙwai a ka, wannan yardar za ta ragu."

Abin da ya sa iyaye ba su fahimta ba

प्रतीकात्मक तस्वीर.

Asalin hoton, GETTY IMAGES

Matsala guda da ke tattare da waɗannan wasannin zolaya ko na tsoratarwa shi ne waɗannan hotunan bidiyo ana naɗa ne sannan a wallafa a shafin intanet ba tare da izinin ƙananan yaran ba.

Abin tambayar shi ne, ta yaya wasannin zolayar da ke iya cutar da yara ya zama abin nishaɗi? Musamman idan yaran da ke cikin bidiyon suka nuna ba su ji daɗin abin ba.

Masaniyar halayyar ƙananan yara Rachel Melville-Thomas ta kuma yi mamaki cewa a waɗannan bidiyon na zolaya, yaran ba sa jin daɗi amma iyayen da masu yin zolayar suna sheƙa dariya.

Hakan ya saɓa da amincewarsu wadda galibin masana halayyar ƙananan yara ke bayar da shawara. Misali, idan yaro ya ji ba daɗi, uwa ma ta kan ji ranta ya sosu. Hakan na taimaka wa yara su san irin halayyar da za su nuna. Amma halayyar da ake gani a wasan zolayar ya yi hannun riga da haka.

Melville-Thomas ta ce "Iyaye na samun ƙarin mabiya idan suka yi irin waɗannan wasannin. A irin wannan yanayin, ba sa tunanin abin da ɗansu zai ji a ransa. Lokacin da suke wasan zolayar, sun fi mayar da hankali kan buƙatunsu a maimakon buƙatun yaran."

Buƙatar a yi tsaka tsan-tsan

प्रतीकात्मक तस्वीर.

Asalin hoton, GETTY IMAGES

Waɗannan wasannin zolayar na iya yin mummunan tasiri kan yara kuma hakan na iya shafar alaƙarsu da iyayensu.

Thomas Melville ta ce a irin wannan yanayin, yana da muhimmanci a yi nazari kan tasirin zolayar a kan yaro. Manufar wasan ba ta da muhimmanci.

Ta ƙara da cewa, "Za ka iya shaida wa yaron cewa bayan da na ga an yi wa wani, sai na yi tunanin na gwada a kanka. Amma yanzu na fahimci cewa bai kamata na yi ba, yi haƙuri."

Yana da muhimmanci a yi haka saboda iyaye sune abin koyi ga ƴaƴansu. Idan ka ce yi haƙuri, kana koyawa ɗanka abin da ya kamata ya yi idan ya yi abin da bai dace ba.

Masanin halayyar ɗan'adam Rajesh Pandey ya ce "Akwai hanyoyi da dama na sanya mutum dariya da nishaɗantar da shi. Idan ka yi zolaya, kana fatan nishaɗantarwa. Amma ba za ka iya gwada tasirin da zolayar za ta yi ba kan wanda aka zolayar."

Ya ce bai da ce a tsoratar ko razanar ko cin zarafin wani ba kawai da sunan nishaɗantarwa. Bai kamata a riƙa yi wa yara har da manya haka ba.