Ko ya kamata yara su ci gaba da karatu a lokacin hutu?

Asalin hoton, Getty Images
Hutun ƙarshen shekara na makarantu ya kankama amma wasu yaran za su ci gaba da karatu da kuma aikin karatu na gida da ake bai wa yara.
Hutun ƙarshen zangon karatu ya kasance lokacin jin dadin ƴan makaranta yayin da za a ajiye jakunkuna da takalman makaranta a wuri guda.
Akan kwashe wadannan kwanaki ana hutu da kuma ziyarar ‘yan’uwa da abokai.
Amma ba duka yara ke samun wannan damar ba, kasancewar akwai darussan da za a so su ƙware a kai kafin a fara zangon karatu mai zuwa.
Wasu iyayen sun yi iƙirarin cewa- me ya sa yara ba za su yi karatu a lokacin hutun ƙarshen zangon karatu ba?
Vivienne Stiles tana koyar da yara daga masu shekara 4 zuwa 16, a lokacin hutu.
Sukan yi karatu sau biyu a mako inda ake basu aikin gida na tsawon tsakanin mintuna 15 zuwa 90 a darussan lissafi da ingilishi.
''Ya kamata a ce ƙwaƙwalwar yara na ci gaba da aiki ko da cikin hutu ne.'' in ji ta.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ta ƙara da cewa, idan suna ɗan yin karatun lokacin hutun za su iya ci gaba da mayar da hankali a karatun da suka yi.
Vivienne - ta ce yaran suna koyon sabbin dabaru da haɓaka ɗabi'ar aiki kuma suna gudanar da tsararrun ayyukan yau da kullun.
Ta ce ƴarta, yanzu ta na da shekara 19 da haihuwa, ta ci gajiyar koyarwar da ake yi ma ta a gida inda har ta sami gurbin karatu a kwalejin kula da lafiyar dabbobi ta Royal Veterinary College da ke birnin Landan,
Mahaifiyar ƴaƴa biyu Tanith Carey ita ma ta kasance babbar mai goyon bayan wannan tsarin karatun.
Amma ta sauya ra'ayi a lokacin da ƴarta ta farko, Lily, ta ƙi karɓar lambar yabon ilimin kimiyya a makaranta a lokacin da ta ke da shekaru bakwai, tana mai cewa ba ta son hayaniya.
Sai a lokacin Tanith ta samu labarin irin matsin lambar da diyarta ke fuskanta.
Don haka, ta dakatar da koyar da lissafin a lokacin hutu, kuma Lily ta samu ƙarin lokaci don ƙara shaƙuwa da kuma kasacewa tare da kanwarta Clio.

Asalin hoton, Tanith Carey
Tanith ta ce, kamar sauran iyaye da dama, ita ma ta bari guguwar tashin hankali ya kwashe ta.
''Gasa tsakanin iyaye yana ta yaɗuwa - saboda suna tsoron idan wani yaro ya wuce gaba a karatu ƴaƴansu za su ji kaman an bar su a baya. Don haka lamarin yana ƙara bazuwa.'' in ji ta
''A tunanina abin takaici ne a ce ana yi wa lokacin hutu ganin kamar ci gaban karatun makarata ne, a matsayin wani lokaci da yara za su yi amfani da shi domin su zarce wa tsararrakinsu a karatu.''
A cikin littafinta, mai suna 'Taming the Tiger Parent', Tanith ta yi rubutu game da ra'ayin tunzura yaro.
Ta bayyana cewa ''Wani abu ne da kowane yaro yake da shi kuma shi ne abu ɗaya da yake son yi kuma yana jin daɗin yin sa.''
"Yaran za su iya gano hakan ne idan an bar su da abin da suka gudanar da al'amuransu."
A lokacin hutun ƙarshen shekara, Clio ƴar shekara 12 ta yanke shawarar cewa za ta fara ɗaukan hotuna ta sanya su a albam, sa'annan ta tattara wasu girke-girken abincin wadanda da ba su cin nama.
Ƴar'uwarta, Lily, wadda yanzu ta ke da shekaru 15, za ta tafi ƙasashen waje don koyon harkar kaɗe-kaɗe - duk da cewa jarabawarta na GCSE na ƙaratowa.
Haka kuma za ta yi maraba da samun ƴancin rashin tashi da safe domin zuwa makaranta, da kuma karanta duk wani littafi da take so, in ji Tanith.
Lokacin hutunta ta yi matuƙar shaƙatawa inda ta yi irin wasannin da ta ke so kuma su ne abubuwan da ta ke tunawa masu faranta ma ta rai a lokacin kuruciyarta.
‘'Ina tsammanin a cikin fargaba da tsoro game da rayuwa, iyaye sukan manta cewa wasanni da zamantakewa na cikin hanyoyi mafi inganci da ake koyon abubuwa, ta hanyar samun ilimin duniya.
"Suna manta cewa yara suna da hanyoyin samun ilimi guda biyu, wanda suka haɗa da makaranta da kuma wanda suka samu daga zamantakewa."

Asalin hoton, Getty Images
Mahaifin ƴaƴa uku kuma marubucin littafi mai suna 'idle parent' Tom Hodgkinson, ya shafe lokacin hutunsa na ƙarshen shekara yana yawo cikin walwala da wuraren shakatawa har ma da wuraren zubar da shara.
Kila ba zai bai wa yara shawarar wasa a cikin shara ba a halin yanzu, amma ya yarda ya ba su sararin yin wasasanni kamar su hawa bishiya da abubuwan da suka jiɓanci hakan.
Yace ‘’Ku bar yara su gudanar da al'amuransu kawai, ku kasance dai a kusa amma ku bar su su ci gaba da harkokinsu.''
Ya ƙara da cewa duk wani fannin rayuwa a tsare ya ke don haka hutun ƙarshen shekarar ya kamata ya zama lokacin rayuwa cikin jin daɗi da yin ƙirƙire-ƙirƙire ba tare da wani mai tsawatarwa yana kewaye-kewaye ba.
Yana koya maka wadatar kai, da ikon nishadantar da kanka da yadda za ka kula da kanka.
"Wadannan dabarun ƙila ba za su yi amfani ba a rayuwar aikin kamfani ba ko kuma idan kana son ka zama ci-ma-zaunen gwamnati amma suna da amfani idan ka na son ka zama wanda ya san ciwon kansa," in ji shi.











