Yaron da ya koya wa kansa karatu tun yana ɗan shekara biyu

Wani yaro wanda ya koya wa kansa yadda zai yi karatu ya zama ɗaya daga cikin ƴaƴan ƙungiyar masu kaifin basira ta ƙasa da ƙasa.
Yaron mai shekara huɗu, shi ne mafi ƙanƙancin shekaru da ya shiga ƙungiyar a Birtaniya.
Teddy, wanda ya fito da Portishead zai iya ƙirga 1-100 da yare shida ciki har da sinanci.
Ƙungiyar masu kaifin basira ta Mensa na karɓar wadanda aka auna kaifin basirarsu da ya kai kashi 98 ko sama da haka a jarabawar kaifin basira da aka amince da ita.
Mahaifiyar Teddy, Beth Hobbs ta bayyana cewa ɗanta ya koyi karatu ne tun yana da watanni 26 da haihuwa ta hanyar kallon shirye-shiryen yara a talabajin inda kuma yake kwaikwayar sautin kalmomi".

"Ya fara bibiyar kalmomi daga nan muka tura shi makaranta bayan kullen korona, mun faɗa masu cewa ya koya wa kansa yadda ake karatu," in ji ta.
"Mun samu kiran waya daga makarantar, waɗanda suka aiko da malamai domin tabbatar da ko ya iya karatu, wanda ya ce, eh! ya iya.

Ɗayan lamarin da ya faru ne ma ya fi bai wa iyayen Teddy mamaki.
"Yana wasa a kan teburin shi, inda yake ta gwalangwalan dinsa da na kasa ganewa, sai na tambaye shi me yake yi, sai ya ce mani Mama ina ƙirga ne da sinanci," in ji Mrs Hobbs

An saka Teddy cikin ƙungiyar Mensa a lokacin da yake da shekara uku da haihuwa, wanda hakan ya sa ya zama mafi ƙarancin shekaru da yake cikin ƙungiyar a Birtaniya.
Iyayen sun kuma bayyana cewa yaron ya soma gano cewa abokansa ba su iya karatu ba amma bai san dalili ba.










