Yaran da suka zama marayun dole bayan ƙaurar iyayensu

Yaro

Asalin hoton, Natalia Favre

Ƙasar Cuba na fuskantar tuɗaɗar jama'a zuwa wasu ƙasashe da nufin ƙaura daga ƙasar.

Sannan matsalolin shugabancin da na tattalin arziki da aka samu sakamakon illar da annobar corona ta yi wa ƙasar ya ƙara munana lamarin, abin da ya tilasta wa 'yan ƙasar da dama barin ƙasashensu domin neman ayyuka a ƙasashen waje.

Matasan Cuba, da matasan ƙwararru masu yawa, musamman na yin ƙaura domin ficewa daga ƙasar.

Dubun dubatar 'yan Cuba ne suka yi ƙaura zuwa Amurka ta kan iyakar Mexico ko ta iyakar ruwa.

Hukumar kula da kan iyakar Amurka ta ce adadin 'yan ƙasar Cuba da ke shiga Amurka ta tashi daga 39,000 a shekarar 2021 zuwa mutum 224,000 a shekarar 2022.

Adadin ya zarta yawan 'yan ƙasar da suka fice daga ƙasar a shekarun 1980 da 1990.

A yayin da tafiyar ke cike da hatsari, da yawa daga cikin masu ƙaurar kan bar 'ya'yansu a Cuba domin tafiya ƙasashen waje domin neman kuɗi.

Tare da fatan cewa wata rana 'ya'yan nasu za su koma ƙasar da suka je domin ci gaba da zama a can, idan suka samu takardun izinin zama, to sai dai hakan kan ɗauki shekaru.

To sai dai kafin hakan, sukan yi ayyuka domin samun kudin da za su aika wa iyalan nasu, domin gudanar da raywarsu.

Mafi yawan yaran da iyayensu suka bari a ƙasar kan rayu a ƙarƙashin kulawar kakanninsu ko 'yan uwan iyayen nasu.

Wani bincike da masana ilimin halayyar dan adam suka gudanar a shekarar 2017 ya nuna cewa yaran da suka taso ƙarƙashin kulawar kakanni ko kawunnai, bayan iyayensu sun fice daga ƙasar, sukan fuskanci yawan fushi da damuwa da jin rashin shaukin kaunar iyaye.

Cataleya Larrinaga Guerra mai shekara tara wadda ke zaune kakanninta tare da kanwarta Caterine mai shekara bakwai a garin Los Pocitos a wani gari na talakawa a yankin Havana.

Yarinya

Asalin hoton, Natalia Favre

Mahaifinsu Vladimir ya bar Cuba a lokacin da Caterine ke wata ɗaya da haihuwa.

Shekaru huɗu bayan nan mahaifiyarsu mai suna Yanet, ta fice daga ƙasar domin tafiya wajen uban 'ya'yan nata wanda ke zaune a Amurka.

Tun daga wancan lokacin Vladimir tare da matarsa Yanet ke zaune a garin Austin na jihar Texas ta Amurka tare da fatan cewa wata rana 'ya'yan nasu za su koma Amurka su same su a can domin ci gaba da rayuwa a matsayin iyali.

Yaran tare da kakansu

Asalin hoton, Natalia Favre

A kowanne wata Vladimir tare da matarsa Yanet kan tura kuɗaɗe daga Amurka zuwa Cuba domin kula da 'ya'yan nasu, tare da kiransu ta bidiyo domin yaran nasu su zaɓi kalar 'yar tsanan da suke so su saya domin aika musu zuwa Cuba.

Yara

Asalin hoton, Natalia Favre

''Abu ne mai matuƙar wahala, suna jin zafin rashin iyaye,'' in ji kakan yaran Alfonso, wanda shi ke kula da yaran.

"Idan wani abu ya faru da ƙaramar , sai ta fara kuka ta riƙa cewa a kai ta wajen mahaifiyarta. Ko da za mu ba ta duka soyayyar duniyar nan, ba kamar iyayenta ba, saboda iyaye, iyaye ne kuma yaran na buƙatarsu,'' in ji Alfonso.

Alfonso ya ce Caterine ta fara kiransa da 'Baba' matarsa kuma 'Umma' sai dai a cewarsa sun sha yi maya bayanin cewa su kakanninta ne, amma nan ba da jimawa ba za a akai su wajen iyayen nasu.

Yara

Asalin hoton, Natalia Favre

Alexander Gonzales León mai shekara 9, wanda ke zauna a wani bene mai hawa biyu a garin Guanabacoa, da ke wajen birnin Havana, shekara uku da suka gabata, iyayensa da kakanninsa da kawunnansa da duka 'yan uwansa na zaune ne a wannan gida.

To amma a yanzu mafi yawan ɗakunan gidan a rufe suke, kuma a yanzu shi kansa Alexander na ƙarƙashin kulawar kanwar mahaifiyarsa mai suna Mercedes. Duka sauran iyalan suhn tafi Amurka.

Yara

Asalin hoton, Natalia Favre

Mahaifiyarsa mai suna Lourdes kan je ƙasashe irin su Guyana ko Panama domin saro kayayyaki, domin sayarwa a ƙasar domin samun kuɗin gudanar da rayuwa.

Wata ranar ta zauna a Mexico sannan ta nemi izini domin ɗan nata ya koma can da zama. To amma hakan bai samu ba.

Domin kuwa a daidai wannan lokacin ne aka rufe kan iyakokin ƙasashe sakamakon annobar Korona, daga nan kuma Lourdes ta ƙara samun cikin ɗanta na biyu a Mexico

Yara

Asalin hoton, Natalia Favre

Mahaifiyar Alexander kan aika da kuɗi duk wata ga Mercedes domin kula da yaron.

Mercedes ta ce "Abinci da tufafi da kayan makaranta, ki komai ma mahaifiyarsa ce ke aiko min da kuɗinsa''.

Mercedes ta ce Alexander ba ya jin zafin rashin mahaifiyar tasa domin kuwa a cewarta kodayaushe yan ganinta a waya idan suna kiran bidiyo.

Haka su ma iyayen Eyko Rodríguez Lara sun bar Cuba a shekarar da ta gabata, inda suka tafi Rasha domin neman kuɗi

Yaro

Asalin hoton, Natalia Favre

A yanzu Ezko na zaune da kanwarsa Elizabeth mai shekara biyu tare da kakanninsu biyu Lourdes da Raisa.

Tsofaffin matan biyu kan yi karɓa-karɓa wajen lura da 'ya'yan kuma suna zaune ne a gida ɗaya.

Yaro

Asalin hoton, Natalia Favre

Bayan da iyayensa suka tafi Rasha a shekarar da ta gabata, Eyko ya fara samun matsaloli masu alaƙa da damuwa.

Inda kakannin nasa suka kai shi wajen likitan ƙwaƙwalwa wanda ya cemasu tunanin iyayensa ne ya janyo masa matsalar da yek ciki.

Eyko ya fara zuwa wani shagon zane-zane a tsakiyar birnin havana domin taimaka masa rage damuwar da yake ciki.

Yaro

Asalin hoton, Natalia Favre

'Yar uwar tasa Elizabeth wadda mai tsananin kunya ce, ta shaƙu matuƙa da kakarta mai suna Lourdes.

Yaro

Asalin hoton, Natalia Favre

Kakannin nasu na cike da fatan cewa iyayen yaran za su samu takardun izinin zama a Rasha nan ba da jimawa ba, domin ɗaukar 'y'yan nasu. To amma sun san hakan zai ɗauki lokaci.

Raisa ta ce 'yarsa ta yi da-na-sanin barin 'ya'yanta. ''Tana matuƙar jin takaicin tafiya ta bar 'ya'yan nata'', in ji ta.