Muhammad ya ƙara zama sunan da aka fi sanya wa jarirai a Ingila da Wales

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, André Rhoden-Paul & James Gregory
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 4
An fitar da sunayen jarirai da suka fi tashe a shekarar 2024 a Ingila da Wales, inda Athena da Yahya suka shiga cikin guda 100 na farko da aka fi sanya wa yara a karon farko.
Muhammad ya zama na ɗaya a ɓangaren maza, shekara biyu ke nan a jere, inda Noah da Oliver suka zo na biyu da na uku, kamar yadda yake a shekara ta 2023.
Olivia da Amelia ne sunayen yara mata na ɗaya da na biyu da aka fi sanyawa, karo na uku a jere, sai dai Isla ya fita daga cikin ukun farko a sunayen da aka fi sanya wa yara mata, inda Lily ya maye gurbinsa.
Ofishin ƙididdiga na Birtaniya ne ya fitar da alƙalumar, wanda shi ne ke tattara bayanan takardar rajistar haihuwa.
Sabbin sunayen yara mata da suka shiga 100 na farko su ne Eloise da Nora da Myla da Rosa da Athena da Sara da kuma Zoe.
A ɓangaren maza kuma akwai Austin da Nathan da Vinnie da kuma Yahya.
Muhammad ya kare kambinsa na sunan da aka sanya wa jarirai maza ne inda aka sanya wa yara 5,721 sunan. Ya zamo sunan da aka sanya wa jarirai a yankuna biyar cikin tara na Ingila, sannan na 57 a Wales.
Haka nan sauran yadda ake rubuta sunan, kamar Mohammed, shi ne na 21 inda aka sa wa jarirai 1,760, sai kuma Mohammad a matsayin na 53, wanda aka sanya wa jarirai 986.
Jarirai mata 2,761 ne aka sanya wa suna Olivia a Ingila da Wales, inda ya zama na ɗaya da ake yayi a yankuna bakwai na Ingila da Wales.

'Iyaye na son sanya wa yaransu sunan da ba a saba ji ba'
SJ Strum, wata ƙwararriya kan lamarin jarirai kuma mawallafiyar wani littafi kan yara, ta ce ba ta ji mamakin yadda sunan ya sake kasancewa na farko a cikin sunayen da ake yayi ba.
Envy, suna ne da kowa ke so - a shekarun 1990 Louise aka fi so, a shekarun 1980 kuma an fi son Sarah," in ji Strum.
"Olivia suna ne mai dadi, amma yanzu ba a fiye sanya sunan ba. Yanzu mutane sun fi son sanya sunan da ya bambanta da saura."
"Iyaye na lura da abubuwan da ke faruwa a inda suke sannan kuma suna bin abin da ransu ke so," kamar yadda ta yi ƙarin bayani.
Sai dai ta ce idan aka koma kan sunayen yara maza, iyaye ƴan Birtaniya na "bin al'ada ne", saboda suna shirya musu "yadda za su gaje su a wurin aiki".
Ta ce sunayen yara da suka yi fice a shekaru da dama da suka gabata, a yanzu suna sake dawowa.
"Yanzu akwai Arthur a cikin 10 na farko - ba haka abin yake ba shekaru 15 da suka gabata."
'Sunaye masu alaƙa da muhalli na samun karɓuwa'
Wata ƙwararriya a fagen sunaye Clare Green, ta ce wannan ne ake ce wa 'salon ƙarni ɗaya'.
Shi ya sa za mu iya ganin wasu sunayen suna dawowa, kamar Susan da Roger, a matsayin wadanda za su yi tashe nan gaba, in ji ta.
Sunaye masu nasaba da yanayi da kuma muhalli sun kasance cikin waɗanda suka fi tashe, inda ake da suna kamar Lily da Poppy da kuma Ivy a cikin 10 na farko.
Green ta ce waɗannan sunaye ne da "ba sa tsufa" - sun kasance cikin 100 da aka fi sanyawa a tsawon shekaru.
To amma ko akwai wani suna da ya ba ta mamaki a wannan karo?
"Ta wani fannin, kamar sunayen da mutane ke ganin sun tsufa, irin su Jessica, amma kuma har yanzu suna a cikin 100 na farko da aka fi sawa," in ji ta.
Sunayen maza da aka sanya wa jarirai da bai fi sau biyar ba a 2024 su ne Awesome da Cuthbert da Crispin da kuma Beckham.
Sunayen mata da su ma ba su kai biyar ba su ne Sicily da Everest da Orchid da kuma Poem.











