Juventus za ta sayo Kane, Paris St-Germain za ta sabunta kwangilar Neymar

Juventus ta mayar da hankalinta wurin dauko dan wasan Tottenham dan Ingila mai shekara 26, Harry Kane. (Corriere dello Sport - in Italian)

Real Madrid ta daina zawarcin Harry Kane saboda matsalolin rashin kudin da ta fada a ciki sakamakon cutar korona. (Mail)

Real Madrid na duba yiwuwar sayar da 'yan wasa shida, cikinsu har da dan wasan Wales Gareth Bale, mai shekara 30, da takwaransa dan kasar Columbia mai shekara 28, James Rodriguez. (AS)

Paris St-Germain na shirin tsawaita kwangilar dan wasan Brazil Neymar zuwa shekara 2025. Za a rika biyan dan wasan mai shekara 28 euro 38m duk shekara. (Sport - in Spanish)

Arsenal za ta iya mika dan wasan Faransa Alexandre Lacazette, mai shekara 28, ga Atletico Madrid a wani bangare na yarjejeniyar dauko dan wasan Ghana Thomas Party, mai shekara 26. (Sun)

Arsenal ta taya dan wasan Valencia da Spaniya mai shekara 29, Rodrigo Moreno. (Mirror)

Arsenal da Manchester United suna duba yiwuwar zawarcin dan wasan Barcelona da Faransa mai shekara 22, Ousmane Dembele. (Sport - in Spanish)

Manchester United ta saka sunan dan wasan Bayer Leverkusen da Jamus Kai Havertz, mai shekara 20, cikin jerin 'yan kwallon da za ta dauko. (Standard)

Chelsea ta ware £20m don sayo dan wasan Freiburg da Jamus mai shekara 23, Luca Waldschmidt. (Sun)

Dan wasan Chelsea da Faransa Olivier Giroud, mai shekara 33, ya amince da yarjejeniya a Inter Milan. (Tuttosport via Mail)

Inter Milan ta shirya bayar da £25m ga dan wasan Everton mai shekara 20 Moise Kean. (Express)

Newcastle za ta kashe £200m a kan sabbin 'yan wasanta da kuma inganta kungiyar idan shirin da ake yi na sayar da ita ya yi nasara. (Mirror)

Derby da Besiktas suna son dauko golan Burnley Joe Hart, mai shekara 33. (Sun)

Anderlecht za ta kori tsohon dan wasan Manchester City da Arsenal Samir Nasri, mai shekara 32, bayan ya gaza tuntubar kungiyar lokacin dokar zaman gidan da aka sanya saboda cutar korona. (Derniere Huere via Mail)