Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An soke bikin karramawa na Gasar Premier kan coronavirus
An soke bikin karramawa na Hall of Fame na Gasar Premier saboda coronavirus.
An tsara kaddamar da 'yan wasa guda biyu a ranar Alhamis a wani biki da aka shirya yi a London, kuma za a bayyana sunayen 'yan takara na gaba da magoya baya za su zaba.
Har yanzu Premier ba ta bayyana tsara sunayen mutanen ba.
An dakatar da duk wasanni a Birtaniya saboda cutar ta Covid-19, har sai ranar 3 ga watan Afrilu mai zuwa.
An tsara cewa kungiyoyin Premier za su tattauna a ranar Alhamis mai zuwa kan hanyoyin da za su bi kan matsalar cutar, biyo bayan hukuncin da Uefa za ta dauka wanda za ta bayyana a ranar Talata.
Shirin gudanar da bikin Hall of Fame na Premier an sanar da shi ne a watan da ya gabata.
Dole ne 'yan takarar ya zama sun yi ritaya daga kwallo, kuma wadanda suka buga gasar Premier a baya.