An soke bikin karramawa na Gasar Premier kan coronavirus

EPL

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An dakatar da duk wasanni a Burtaniya saboda cutar ta Covid-19, har sai ranar 3 ga watan Afrilu mai zuwa

An soke bikin karramawa na Hall of Fame na Gasar Premier saboda coronavirus.

An tsara kaddamar da 'yan wasa guda biyu a ranar Alhamis a wani biki da aka shirya yi a London, kuma za a bayyana sunayen 'yan takara na gaba da magoya baya za su zaba.

Har yanzu Premier ba ta bayyana tsara sunayen mutanen ba.

An dakatar da duk wasanni a Birtaniya saboda cutar ta Covid-19, har sai ranar 3 ga watan Afrilu mai zuwa.

An tsara cewa kungiyoyin Premier za su tattauna a ranar Alhamis mai zuwa kan hanyoyin da za su bi kan matsalar cutar, biyo bayan hukuncin da Uefa za ta dauka wanda za ta bayyana a ranar Talata.

Shirin gudanar da bikin Hall of Fame na Premier an sanar da shi ne a watan da ya gabata.

Dole ne 'yan takarar ya zama sun yi ritaya daga kwallo, kuma wadanda suka buga gasar Premier a baya.