Makomar Ighalo, Van de Beek, Ronaldo, De Bruyne, Sterling da Kane

Harry Kane na Tottenham

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasan Manchester United da Najeriya Odion Ighalo, mai shekara 30, wanda ya zo a matsayin aro daga Shanghai Shenhua, a shirye yake ya amince a datse albashinsa kusan fam miliyan £6 don ci gaba da taka leda a Old Trafford. (Mail)

Manchester United na son karbo dan wasan Ajax Donny van de Beek, dan wasan tsakiya da Real Madrid ta nuna sha'awar tana so. (Marca - in Spanish)

Juventus na shirin sabunta kwanglar Cristiano Ronaldo, mai shekara 35, inda zai ci gaba da taka leda a kulub din na Seria A har 2024. (Tuttosport via Mail)

Dan wasan gaba na Ingila da Tottenham Harry Kane, mai shekara 26, ya fi kaunar ya koma Manchester United ko Manchester City maimakon ya koma Juventus. (Tuttosport via Express)

Manchester City za ta yi amfani da damar da ta samu na dage wasannin Premier domin tattaunawa da dan wasanta Kevin De Bruyne, mai shekara 28, kan sabunta kwanglar shi da kuma dan wasan Ingila Raheem Sterling, mai shekara 25. (Sun)

Kocin Arsenal Mikel Arteta yana son dan wasan West Ham Issa Diop, mai shekara 23da aka bayyana darajarsa ta kai kudi fam miliyan£60 wanda kuma Manchester Unitedke ra'ayi. (Metro)

Dan wasan gaba naBirmingham City Jude Bellingham kungiyar da zai koma tsakanin - Manchester United, Chelsea, Bayern Munich da Borussia Dortmund - wadanda a shirye suke su biya fam miliyan £30 kan dan wasan na Ingila mai shekara 16. (Sun)

Barcelona, Manchester United da Real Madrid na hamayya kan dan wasan Fenerbahceta Turkiya Omer Beyaz, mai shekara 16. (Express)

Golan Sheffield United Dean Henderson, mai shekara 23, ana tunanin zai koma tsohuwar kungiyarsa Manchester United duk da sha'awar shi da Chelseata nuna (Star)

'Yan wasa da dama da suka ji rauni a Turai za su more dage wasannin da aka da yi saboda cutar coronavirus domin ba su damar su murmure. (Mail)