Tinubu ya ce ana kassara APC saboda zaben 2023

Asiwaju Bola Tinubu

Asalin hoton, @AsiwajuTinubu

Jagoran jam'iyyar APC na kasa Asiwaju Bola Tinubu ya ce wadanda ke neman a cire Adams Oshiomole daga mukamin shugaban jam'iyyar "zazzabin 2023" ne ke damun su.

Jagoran jam'iyyar ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya saka wa hannu ranar Lahadi, inda ya ce ya zama wajibi 'yan jam'iyyar su hada hannu "domin kawar da wata cuta" a cikin jam'iyyar.

"Wata dadaddiyar cuta ce ta bukatar 2023, wadda ta damu wasu 'yan siyasa da kuma abokansu 'yan jarida," Tinubu ya bayyana a sanarwar.

A kwanakin baya rahotanni suka ambato kungiyar gwamnonin APC tana kiran kwamitin gudanarwar jam'iyyar na kasa da ya sauke Oshiomole daga mukaminsa, inda suka goyi bayan hukuncin wata kotu a Abuja.

Sai dai Oshionole ya daukaka kara a wata a Jihar Kano, wadda ta dakatar da aiwatar da hukuncin sauke shin.

Rashin jituwa tsakanin gwamnonin APC da kuma shugabancin jam'iyyar na kasa karkashin Adams Oshiomole ya janyo rabuwar kai a jam'iyyar.

Wannan ta sa masharhanta irinsu Dakta Abubakar Umar Kari na Jami'ar Abuja ke ganin har yanzu "APC ba ta zama cikakkiyar jam'iyya ba".

Tinubu ya ce wadanda ke nuna waccan bukata so suke su samu damar juya akalar jam'iyyar da fara fafatawa shekara uku kafin zaben 2023.

"A yanzu duk abin da suke yi ko suke cewa ya ta'allaka ne kan mukami da kuma iirn tasirin da za su yi a sakamakon zaben 2023 shekara uku kafin ya zo.

"A yunkurinsu na yin hakan, sai kuma suke kokarin yin zagon kasa ga jam'iyyar da suke ikirarin suna yi wa biyayya da kuma gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari."

Ya kara da cewa "suna so ne su fara yin tsere a kan titin da ko gina shi ma ba a yi ba".

Wannan kalamai nasa na zuwa ne yayin da jam'iyyar ke ci gaba da jiran hukuncin karar da Adams Oshiomole ya daukaka.

Sakatariyar APC
Bayanan hoto, Ana yi wa sakatariyar APC kwaskwarima yayin da ake shirin yin taron kwamitin gudanarwar ranar Talata

Sai dai a ziyarar da wakilin BBC ya kai ofishin jam'iyyar ranar Lahadi, ya tarar ana ta aikin gyaranta, a wani bangare na shirin da ake yi na taron kwamitin gudanarwar jam'iyyar ranar Talata.

Sakatariyar APC

Asalin hoton, BBC

'Har yanzu ba ta zama cikakkiyar jam'iyya ba'

Buhari da Tinubu

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto, Tinubu yana da tasiri sosai a jam'iyyar mai mulki kuma ya taimaka wa Shugaba Buhari wurin cin zabe a 2015 da 2019

"Muna fada muna nanatawa cewa har yanzu APC ba ta zama cikakkiyar jam'iyya ba, gungu-gungu ne na mutane da ke da akidu daban-daban wadanda a baya ma fada suke yi da juna," in ji Dakta Abubakar Umar Kari, masanin kimiyyar siyasa a Jami'ar Abuja.

Ya kara da cewa abin da kawai ya hada 'yan jam'iyyar APC shi ne "wata dama da za su karbi mulki a shekarar 2015".

Jam'iyyar APC dai ta kafu ne bayan jam'iyyun AC da CPC da ANPP da wani bangare na APGA sun dunkule kafin a shiga babban zaben 2015, abin da ya sa suka kwace mulki daga hannun jam'iyyar PDP da dan takararta Shugaba Goodluck Jonathan.

"Idan irin wannan rikici ya ci gaba abubuwa da dama za su iya faruwa da ita (APC), wadansu ma na ganin za ta iya wargajewa," Kari ya fada.

"Ko da haka ba ta faru ba to ina ganin kwarjininta zai ragu kwarai da gaske."

Dakta Kari ya ce tabbas a siyasa ba a rasa yadda za a yi wurin gyara matsaloli, sai dai yana ganin cewa halin ko-in-kula na Shugaba Buhari a matsayinsa na jagora zai iya kawo tsaiko wurin saita jam'iyyar.

"Shugaba Muhammadu yana da hailin ko-in-kula, ba shi da niyyar a sasanta, ba ya wani katabus, kuma ba abin mamaki ba ne idan halin nasa ya ci gaba."