Ana sa ran kammala Champions League na kakar nan ranar 29 ga Agusta

    • Marubuci, Simon Stone
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai na tsara yadda za a kammala gasar Champions League ta kakar 2019-20 ranar 29 ga watan Agusta.

A ranar 23 ga watan Afirilu hukumar za ta tattauna kan yadda za ta kammala wasannin bana da cutar korona ta kawo tsaiko.

Wata shawara ita ce watakila a kammala gasar da wuri kan lokacin da ake son cimma, amma dai sai Uefa ta amince da duk wata shawara kan a aiwatar.

Amma dai fatan shi ne a kammala kakar bana gabaki daya a karshen watan Agusta, har da buga kwantan wasannin da suka rage.

Uefa na sa ran karkare wasan karshe a Champions League a Istanbul ranar 29 ga watan Agusta da kuma na Europa League ranar 26 ga watan Agustan.

Sai dai kuma a kwai matsala biyu da za a fuskanta, saboda haka ya kamata a zabi guda don samun hanyar da za a karkare wasannin Zakarun Turai na shekarar nan.

Na farko dai a buga wasannin daf da na kusa da na karshe gida da waje a Yulii da Agusta.

Ko kuma a buga karawar da suka rage a matakin karamar gasa da za a hada kungiyoyin wuri guda domin fidda gwani.

Sai dai kuma an buga wasa hudu daga takwas a karawar daf da na kusa da na karshe, da wasan da Real Madrid za ta ziyarci Manchester City wadda ta ci wasan farko a Spaniya.

A wasannin Europa ne ake da kalubale babba, inda dukkan karawar wasannin kungiyoyi 16 da suka rage za a buga su da kuma wasa biyu tsakanin kungiyoyin Spaniya da na Italiya da ba su buga karawa ko daya ba.