An yi wa Buhari ihu, coronavirus ta shiga Najeriya

    • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
  • Lokacin karatu: Minti 5

Masu iya magana kan ce waiwaye adon tafiya, a kwana a tashi ba wuya domin har Fabrairun 2020 ta kawo karshe. Sai dai a cikin watan na Fabrairun, abubuwa da dama sun faru wadanda suka ja hankalin 'yan kasar da ma duniya baki daya.

Sai dai mun duba muhimmai daga cikin wadannan abubuwa wadanda suka faru tun daga farko zuwa karshen wannan wata.

Abu na farko da za a iya cewa ya ja hankalin 'yan kasar bayan shiga wannan wata shi ne batun harin da 'yan sandan kasar suka kai wa kungiyar 'yan bindiga ta Ansaru a Kaduna kuma har hakan yayi sanadiyar harbo jirgi mai saukar ungulu na 'yan sandan. Duba kasa domin karanta cikakken labarin da ma wasu labaran.

An harbo jirgin 'yan sanda, an kashe 'yan bindiga 250 a Kaduna

.

Asalin hoton, NIGERIA POLICE

A farkon watan Fabrairu ne rundunar 'yan sandan Najeriya mai yaki da 'yan fashi ta Operation Puff Adder ta ce ta kai samame wani sansanin kungiyar 'yan bindiga ta Ansaru, inda ta kashe 250 daga cikinsu.

Sai dai a yayin kai samamen, an harbi wani jirginta mai saukar ungulu a lokacin samamen.

'Yan sandan sun kai samamen ne a dajin Kuduru da ke Birnin Gwari a jihar Kaduna a safiyar ranar Laraba 5 ga watan Fabrairu, tare da taimakon sojojin sama.

Sai dai tun bayan wannan samame, babu wani cikakken karin bayani dangane da gawarwakin 'yan bindiga 250 da rundunar ke ikirarin ta salwantar.

Boko Haram ta kashe mutum 30 a Borno

.

Asalin hoton, BORNO GOVT

A ranar Lahadi, 9 ga watan Fabrairun 2020 ne wasu da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne suka halaka mutum fiye da 30 a garin Auno na jihar Borno.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:00 na dare kamar yadda dan majalisar wakilai Satomi Ahmad ya shaida wa BBC.

'Yan bindigar sun kona motoci kusan 20 kuma wasu akwai mutane a cikinsu, sannan kuma akwai mata da kananan yara a cikin wadanda suka yi awon gaba da su.

Auno shi ne garin da shingayen jami'an tsaro suke na karshe wanda daga shi sai shiga birnin Maiduguri.

An yi wa Buhari ihu a ziyararsa ta Maiduguri

.

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

Kwanaki kadan bayan harin da aka kai a garin Auno na Maiduguri, Shugaban Najeriya ya kai ziyarar jihar Borno bayan dawowarsa daga Addis Ababa.

Yayin wannan ziyarar,an yi wa shugaban ihun ''ba ma yi, ba ma yi''.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Hakan kuma ya faru ne lokacin da Buhari yake barin fadar Shehun Borno zuwa gidan gwamna a wani waje da ake cewa 'Yan Nono.

Fadara shugaban kasar ta tabbatar da faruwan hakan inda mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba Shehu ya ce da kunnen shi ya ji wannan ihun sai dai ya yi zargin cewa kila wasu 'yan siyasa ne suka tattaro wasu tsiraru aka ba su kudi don su yi wa Buhari Ihu.

Kotun koli ta soke zaben gwamnan Bayelsa na APC

.

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

A ranar Alhamis 13 ga watan Fabrairu ne Kotun Kolin Najeriya ta soke zaben gwamnan jihar Bayelsa da ke kudu maso kudancin kasar.

Kotun ta soke zaben David Lyon, na jam'iyyar APC mai mulkin kasar ne kwana guda kafin ya sha rantsuwar kama aiki.

Alkalan kotun biyar, wadanda Mai shari'a Mary Odili ta jagoranta wajen yanke hukuncin, sun ce an soke zaben Mista Lyon ne saboda mataimakinsa Biobarakuma Degi-Eremienyo ya mika wa hukumar zaben kasar takardun bogi domin a bar shi ya tsaya takara a zaben ranar 16 ga watan Nuwambar da ya gabata.

Kwana daya bayan hukuncin kotun, hukumar INEC ta mika wa Mista Douye Diri na jam'iyyar PDP takardar shaidar lashe zabe inda jim kadan bayan hakan aka rantsar da shi.

'Baraka ta kunno kai a fadar Shugaba Buhari kan tsaro'

.

Yayin da watan Fabrairu yayi nisa ya kai tsakiya, an samu wata baraka da ta kunno kai a fadar shugaban Najeriya.

Hakan ya faru ne bayan mai bai wa shugaban kasar shawara a kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, ya zargi shugaban ma`aikata a fadar, Abba Kyari da yin shisshigi a cikin al`amuran da suka shafi tsaro.

Manjo-Janar Monguno mai ritaya ya ce katsalandan din da Abba Kyari ke yi a aikinsa ya takaita nasarorin da ake samu a kokarin inganta tsaro a Najeriya.

Babu dai wani martani daga bangaren shugaban ma'aikatan.

Manjo-Janar Monguno ya yi wannan zargin ne a cikin wata wasikar da ya aike wa hafsoshin tsaron kasar tun a watan Disambar 2019.

Taron sake fasalin iyali a Musulunci a Najeriya

.

Asalin hoton, BUHARI SALLAU

A ranar Alhamis 20 ga watan Fabrairu ne aka gudanar da taron sake fasalin iyali a Musulunci a Najeriya wanda aka shirya karkashin jagorancin Majalisar Koli ta addinin Musulunci da hadin gwiwar Gidauniyar Aisha Buhari ta Future Assured.

Daga cikin mahalarta taron akwai Shugaba Buhari da matarsa Aisha Buhari da shugaban majalisar dattijai Ahmad Lawal.

Taken taron dai shi "Sake Fasalin Zamantakewar Aure Domin Cigaban Najeriya,"

Yayin wannan taro, mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga gwamnonin jihohin Najeriya da su kirkiro da wata doka wacce za ta rage yawan mace-macen aure, da kuma kawo karshen fitintunun aure a tsakanin 'yan kasar.

Domin ganin wasu daga cikin hotunan wannan taron, ku latsa nan.

Najeriya ta tabbatar da bullar Coronavirus a Lagos

.

Asalin hoton, Getty Images

A ranar 28 ga watan Fabrairu ne hukumomi a Najeriya suka tabbatar da bullar cutar coronavirus da ake kira Covid-19 a jihar Legas.

Ma'aikatar lafiya ce ta tabbatar da bullar cutar a sanarwar da ta wallafa a Twitter, inda ta ce a karon farko an samu bullar cutar a Najeriya tun barkewarta a China a watan Janairun 2020.

A sanarwar da ya fitar, ministan lafiya na Najeriya Dakta Osagie Ehanire ya ce wani dan Italiya ne da ke aiki a kasar ya shigo da cutar bayan ya dawo daga Milan zuwa Lagos.

Tuni dama hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce cutar coronavirus ta kai wani matsayi na zama annoba a duniya saboda yadda take yaduwa.

Takaddama tsakanin Baban Chinedu da hukumar fina-finai ta Kano kan marigayi Ibro

.

A bangaren nishadi kuma, takkadama ce ta kunno kai a Kannywood tsakanin Yusuf Haruna, wanda aka fi sani da Baban Chinedu da kuma shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano wato Isma'il Na'abba Afakallah.

Takaddamar ta samo asali ne bayan da aka aike wa Baban Chinedu wata takarda a kan wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram yana zargin cewa gwamnatin Kano ta bai wa shugaban hukumar tace fina-finan N5m domin mika su ga iyalan marigayi Rabilu Musa Ibro.

Baban Chinedu dai makusancin Ibro ne, kuma ya ce gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta bai wa Isma'il Na'abba Afakallah kudin ne a matsayin gudunmuwar bikin 'yar gidan marigayi Ibro kusan shekaru biyu da suka wuce.

Sai dai Afakallah ya musanta wannan zargin kuma lauyoyinsa sun bukaci Baban Chinedu ya janye kalaman da ya yi a bidiyon ko kuma a gurfanar da shi a gaban kuliya.