Yadda 'yan sanda suka kashe 'yan bindiga biyar a Katsina

Bayanan sauti'Yan sanda sun yi bata kashi da 'barayi' a Katsina

Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraron karin bayanin da SP Gambo Isa ya yi wa Ishaq Khalid.

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Katsina ta tabbatar da kwato alburusai da bindigogi da kuma kashe wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane biyar a jihar.

Kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar ta Katsina, SP Gambo Isa ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin.

A sanarwar da 'yan sandan suka fitar, sun bayyana cewa wadanda ake zargin sun addabi kananan hukumomin Malumfashi da Faskari da Dandume da Bakori da Kankara da kuma Sabuwa da ke jihar ta Katsina.

Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata.

'Yan sandan dai sun rutsa masu garkuwar ne a dai-dai Mararabar Kankara a hanyarsu ta zuwa Gwarzo da ke jihar Kano domin aikata fashi da makami, kamar yadda wata sanarwa ta bayyana, wadda kwamishinan 'yan sandan jihar Sanusi Buba ya fitar.

'Yan sandan sun tabbatar da kama mutum biyar daga cikin wadanda ake zargin kuma dukkansu sun fito ne daga kananan hukumomin jihar Katsina.

Yayin artabu tsakanin 'yan sanda da barayin, 'yan sandan sun samu nasarar kwato jigida hudu dauke da alburusai 94. Sun kuma kwato bindigogi kirar AK 47 biyu da aka boye a dajin Mararabar Maigora.

Matsalar garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa na kara karuwa a jihar Katsina da kuma wasu jihohi da ke makwabtaka da ita.

Ko a kwanakin baya sai da 'yan bindiga suka kashe mutum 30 a yankin karamar hukumar Batsari a jihar.

Haka ma a watan Janairun bana, 'yan bindigar sun yi awon gaba da fasinjoji kimanin 30 a karamar hukumar ta Batsari.

Kwanaki kadan kafin awon gaba da fasinjojin, sai da 'yan bindigar suka yi garkuwa da wasu jami'an kwastam guda biyu a wani shinge da ke kauyen Dan-bedi a yankin karamar hukumar Jibiya ta jihar Katsina mai iyaka da Jamhuriyar Nijar.