Hotunan taron sake fasalin iyali a Musulunci a Najeriya

An gudanar da taron na sake fasalin iyali a Musulunci a ranar Alhamis ne a Abuja babban birnin Najeriya.

An shirya taron ne domin ci gaban kasa karkashin jagorancin Majalisar Koli ta addinin Musulunci da hadin gwiwar Gidauniyar Aisha Buhari ta Future Assured suka shirya.

Hotunan taron sake fasalin iyali a Musulunci a Najeriya

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto, Daga cikin mahalarta taron akwai Shugaba Buhari da matarsa Aisha Buhari da shugaban majalisar dattajai Ahmad Lawal.
Hotunan taron sake fasalin iyali a Musulunci a Najeriya

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto, Gidauniyar Aisha Buhari ta Future Assured na daga cikin wadanda suka shirya taron.
Hotunan taron sake fasalin iyali a Musulunci a Najeriya

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto, Shugaba Buhari ya yi kira ga Malaman addinan Musulunci da na Kirista da su mayar da hankali kan yin wa'azi a kan zamantakewar iyali.
Hotunan taron sake fasalin iyali a Musulunci a Najeriya

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II na daga cikin wadanda suka yi jawabi mai tsayi. A nan ga dukkan alamu yana yin raha ne da Sarkin Musulmai Sultan Sa'ad Abubabakar da Shugaba Buhari da Oni na Ife.
Hotunan taron sake fasalin iyali a Musulunci a Najeriya

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto, Wasu daga cikin manyan malaman kasar da sarakunan gargajiya sun halarci taron.
Hotunan taron sake fasalin iyali a Musulunci a Najeriya

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto, Sarki Sanusi ya yi kira ga gwamnonin jihohin kasar da su kirkiro da wata doka wacce za ta rage yawan mace-macen aure, da kuma kawo karshen fitintunun aure a tsakanin 'yan kasar.
Hotunan taron sake fasalin iyali a Musulunci a Najeriya

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto, Oni na Ife, Mai Martaba Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, ya ce an jima ana ruwa kasa tana shanyewa, don haka lokacin maganar fatar baki ya wuce.
Hotunan taron sake fasalin iyali a Musulunci a Najeriya

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto, Shugaba Buhari yana gaisawa da Gwamna Babagana Umara Zulum na Borno bayan kammala taron.
Hotunan taron sake fasalin iyali a Musulunci a Najeriya

Asalin hoton, Buhari Sallau

Hotunan taron sake fasalin iyali a Musulunci a Najeriya

Asalin hoton, Buhari Sallau