Erik ten Hag: Man United ta tattauna da kocin Ajax

Ajax coach Erik ten Hag

Asalin hoton, EPA

Manchester United ta tattauna da kocin Ajax, Erik ten Hag, kan damka masa ragamar kungiyar da ke Old Trafford.

Ralf Rangnick ne ke aikin kociyan United a matakin rikon kwarya zuwa karshen kakar bana a yanzu haka, tun bayan sallamar Ole Gunnar Solskjaer a watan Nuwamba.

Sai dai wasu a Old Trafford na ganin ya yi wuri a fara batun wanda za a nada kocin United, koda yake kungiyar na fatan kammala batun daukar mai horarwa da sauri.

Shima kocin Paris St Germain, Mauricio Pochettino yana daga cikin wadanda za a tuntuba, don yi masa tayin aikin.

Kocin Sevilla, Julen Lopetegui yana son kocin United tare da mai horar da tawagar Sifaniya, Luis Enrique, koda yake idan ya tsawaita yarjejeniya da Sifaniya kafin gasar kofin duniya, ba zai iya aikin ba.

Haka kuma United tana bibiyar halin da Chelsea ke ciki, watakila ta yi wa Thomas Tuchel tayi, koda yake bai bayyana cewar yana shirin barin kungiyar ta Stamford Bridge ba.

Ten Hag wanda ya yi mataimakin koci a Bayern Munich yana tare da Ajax tun Disambar 2017 ya kuma kai kungiyar karawar karshe a Champions League a 2019.

Sai dai a bana kungiyar ta Netherlands ta kasa kai bantenta, bayan da aka yi waje da ita a wasannin zagaye na biyu a gasar ta Zakarun Tutai.

Ajax, ta lashe Dutch league a 2019 da 2021, yanzu tana jan ragamar teburin kakar bana da tazarar maki biyu tsakaninta da PSV Eindhoven mai biye da ita.

Duk wanda zai karbi aikin United zai kwan da sanin cewar sai ya sayo fitattun 'yan wasa, bayan da kwantiragin wasu manyan 'yan kwallon zai kare a karshen kakar bana.

'Yan wasan sun hada da Paul Pogba da Jesse Lingard da Edinson Cavani da kuma Juan Mata.