Manchester United ta naɗa Ralf Rangnick matsayin sabon koci riƙon ƙwarya

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta sanar da naɗa Ralf Rangnick a matsayin kocinta na riƙon ƙwarya zuwa ƙarshen kaka, kafin ya samu biza.
Kocin mai shekara 63 ya gaji Ole Gunnar Solskjaer, wanda aka kora a ranar 21 ga watan Nuwamba bayan kashin da United ta sha hannun Watford.
Rangnick ya rabu da aikinsa na shugaban ci gaban wasanni a ƙungiyar Lokomotiv Moscow ta Rasha ya karbi aikin Manchester United.
"Na yi farin cikin karɓar aikin Manchester United kuma zan mayar da hankali ga samun nasara a wannan kakar," in ji Rangnick
Bayan kammala kaka, Rangnick zai ci gaba da zama a Old Traffrod na tsawon shekara biyu a matsayin jami'in tuntuɓa.
Wasansa na farko a matsayin kocin Manchester da ke matsayi na takwas a teburin Premier, zai kasance da Arsenal a ranar biyu ga watan Disamba idan har ya samu biza.
Idan ba haka ba Michael Carrick kocin wuccin gadi zai ci gaba da horar da ƙungiyar.
Ana ganin Rangnick ya taka rawa lokacin da yana aiki a Jamus, inda kocin Liverpool da Jurgen Klopp da na Chelsea Thomas Tuchel duka suka bayyana ƙwarin gwuiwa game da shi.
Ya jagoranci Ulm haurowa zuwa Bundesliga a karon farko kafin ya jagoranci Stuttgart da Hannover da Hoffenheim da Schalke da kuma RB Leipzig.
Ya lashew kofin Jamus da Schalke a 2011 sannan ya jagoranci RB Leipzig zuwa wasan ƙarshe a 2019.
A kakar 2010-11 ya taimakawa Schalke zuwa wasan kusa da ƙarshe a gasar cin kofin zakarun turai kafin ta sha kashi hannun Manchester United 6-1 o











