Jesse Lingard: West Ham ta dauki aron dan wasan Man Utd bayan sayen Said Benrahma

Asalin hoton, Getty Images
West Ham ta dauki aron dan wasan Manchester United Jesse Lingard zuwa karshen kakar wasa ta bana, bayan ta kammala sayen Said Benrahma.
Dan wasan na Ingila Lingard, wanda ya ci kwallaye 33 a wasanni 210 da ya murza wa United, sau uku kacal aka sanya shi a tamaula a wannan kakar wasan.
Kocin United Ole Gunnar Solskjaer ya ce yana son dan wasan mai shekara 28 ya koma Old Trafford "idan ya samu karin kwarewa".
"Ina cike da farin ciki," in ji Lingard. "Wannan sabon babi ne a rayuwata."
Ya kara da cewa: "Babu abin da yake da tabbas amma dai na zo nan ne domin na yi aiki tukuru kuma na taimaka wa kungiyar da irin kwarewata. Wannan si ne babban burina. Ina so na ji dadin buga tamaula sannan na koma buga wasa yadda ya kamata."
West Ham ta so ta mayar da aron Benrahma ya zama ta saye shi dindindin daga Brentford a bazara sai dai ta dauki matakin da wuri inda ranar Juma'a ta saye shi a kan £30m domin ta samu gurbin karbar aron Lingard.
Dokar Premier League ta bai wa kungiyoyi damar daukar aron 'yan wasan biyu ne kacal a cikin gida; West Ham ta kuma karbi aron Craig Dawson daga Watford.
Dan kasar Algeria Benrahma ya tafi London Stadium a matsayin aro daga Brentford a watan Oktoba, a wata yarjejeniya da ta bukaci Hammers ta saye shi a kan £25m da kuma karin £5m a matsayin kudin tsarabe-tsaraben dan wasan.
Dan wasan mai shekara 25 zai zauna a kungiyar zuwa 2026.
Lingard ya sake haduwa da tsohon kocin Manchester United David Moyes a West Ham.











