Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Long, Mbappe, Alli, Rose, Gray, Ramos, Alaba

Aaron Long

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Aaron Long

Liverpool na son ɗauko Aaron Long. ɗan wasan baya na New York Red Bulls da Amurka mai shekara 28. (ESPN)

Real Madrid za ta yi samame zuwa Paris St-Germainko sa yi sa'ar ɗauko Kylian Mbappe, dan wasan Faransa mai shekara 22. (Marca)

Paris St-Germain ta ƙosa ta haɗa Mauricio Pochettino da Dele Alli, ɗan wasan Tottenham mai shekara 24, inda ta ke fatan ɗan wasan zai so ya tsawaita zamansa da zarar ya ɗanɗana rayuwar ƙungiyar. (Eurosport)

Ƙungyar kwallo ta Turkiyya Trabzonspor na cewa ta cimma yarjejeniya da Danny Rose, ɗan wasan baya na Tottenham da Ingila mai shekara 30. (Talksport)

Ɗan wasan gefe na Leicester City da Ingila Demarai Gray mai shekara 24, ya amince ya koma Bayer Leverkusen amma ba a kammala sasantawa kan yawan kudin da za a biya ba.. (Bild - in

Ɗan wasan baya na Spaniya Sergio Ramos mai shekara 34 bai sabunta kwantirahinsa da Real Madrid ba tukuna, wata guda bayan da su ka fara tattunawa domin kwantiraginsa ta yanzu za ta kare a bana. (Marca)

Manchester City ta kusa ɗauko Kayky and Metinho, ƴan wasan Brazil biyu daga Fluminensewadanda duka ke da shekaru 17, kan fam miliyan 9. (Goal)

Manchester City ta ce ta janye sha'awar da ta ke da ita kan David Alaba, dan wasan baya na Bayern Munich da Austria mai shekara 28 a wannan kakar wasa, har ma da kakr wasa na baɗi. (Manchester Evening News)

Southampton na ƙoƙarin ɗauko Ainsley Maitland-Niles ɗan wasan Ingila mai shekara 23 daga Arsenal kafin a rufe kasuwar ƴan wasa na Janairu a ranar Litinin mai zuwa. (Sun)

West Brom ma ta bayyana sha'awarta ta sayen Maitland-Niles, wanda ke son a riƙa ba shi damar buga wasanni a kai a kai. (Mail)