Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Lingard, Pogba, Alli, Garcia, Messi, Yedlin da Tuchel

Jesse Lingard

Asalin hoton, Getty Images

Kungiyar West Ham na iya daina bibiyar batun sayo sabon ɗan wasan gaba idan za su samu damar ɗauko Jesse Lingard, ɗan wasan Ingila, kuma ɗan Manchester United mai shekara 28. (The Athletic - subscription required)

Dan wasan tsakiya na Faransa Paul Pogba mai shekara 27 ya ce zai tattauna da Manchester United a ƙarshen kakar wasan nan domin warware batun zamansa a Old Trafford. (Mail)

Manchester United na ci gaba da sa ido kan Christoph Baumgartner, dan wasan tsakiya na Austria da kungiyar Hoffenheim mai shekara 21. (Sun)

West Brom ta amince da kulla yarjejeniyar ɗauko Mbaye Diagne mai shekara 29, dan wasan gaba na Galatasaray, amma a matsayin dan aro. (Express & Star)

Dan wasan Tottenham Dele Alli a shirye yake ya koma Paris St-Germain, amma shugaban Spurs Daniel Levy ba ya son kyale dan wasan mai shekara 24 ya tafi. (ESPN)

Amma idan Spurs su ka kyale Alli ya tafi, to suna iya neman Florian Neuhaus, dan wasan Borussia Monchengladbach mai shekara 23. (Mirror)

Tottenham na sa ido kan Nikola Maksimovic, mai shekara 29 dan Serbia da Napoli. (Sun)

Manchester City ta amince ta sayar wa Barcelona Eric Garcia, dan wasan baya mai shekara 20. (Goal)

Galatasaray ta taya Yedlin, dan wasa mai shekara 27. (ESPN)

Sabon kocin Chelsea Thomas Tuchel ya tafi Landan da masu taimaka ma sa Arno Michels, kuma koci Zsolt Low zai same shi a Stamford Bridge. (London Evening Standard)

Brighton da Swansea na cikin kugiyoyin da keson daukar dan wasan MK Dons Matthew Sorinola, mai shekara 19 dan kasar Ingila. (Football League World)