Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Di Maria, Upamecano, Garcia, Zirkzee, Tarkowski da Benteke

Di Maria

Asalin hoton, Getty Images

Tottenham ta tuntubi dan wasan Paris St-Germain dan kasar Argentina Angel di Maria a kan yiwuwar daukarsa. Tsohon dan wasan na Manchester United, mai shekara 32, zai samu damar barin PSG a bazara. (L'Equipe via Talksport)

Har yanzuPSG tana sa ran karbar aron dan wasanTottenham da Ingila Dele Alli, mai shekara 24, domin kammala ragowar kakar wasan bana. Spurs na duba yiwuwar daukar dan wasan Borussia Monchengladbach da Jamus Florian Neuhaus, mai shekara 23, a matsayin wanda zai maye gurbinsa. (Mirror)

Kazalika ana hasashen cewa Spurs za ta dauki dan wasan Napoli da Serbia Nikola Maksimovic, mai shekara 29, wanda kwangilarsa za ta kare a karshen kakar wasan bana. (Spazio Napoli via Sport Witness)

Rahotanni na cewa Thomas Tuchel ya soma tsara yadda makomarsa za ta kasance a matsayin kocin Chelsea. Dan kasar ta Jamus, wanda ya maye gurbin Frank Lampard a Stamford Bridge ranar Talata, yana son mayar da hankali wajen daukar dan wasan RB Leipzig da Faransa Dayot Upamecano, mai shekara 22. (SportBild via Team Talk)

Korar da aka yi wa Lampard daga aiki ta karfafa gwiwar West Ham bisa tunanin cewa Chelsea za ta daina zawarcin dan wasan na Ingila mai shekara 22. (Telegraph, subscription required)

Dan wasanChelsea Baba Rahman yana shirin zama dan kwallon farko da zai kama gabansa bayan korar Lampard, a yayin da ake tunanin dan wasan na Ghana, mai shekara 26, zai tafi aro a kungiyar da ke Girka PAOK Salonika . (Sport24 via London.Football)

Dan wasan Manchester United Facundo Pellistri yana shirin barin Old Trafford domin zaman aro yayin da rahotanni ke cewa Club Bruges da Alaves suna son dan wasan mai shekara 19 dan kasar Uruguay, wanda ya je Red Devils daga Penarol a watan Oktoba. (Goal)

Ana sa ran dan wasan Belgium Christian Benteke, mai shekara 30, zai zauna a Crystal Palace duk da sha'awar daWest Bromwich Albion ke yi ta daukarsa.(Sky Sports)

Leicester City na kara samun kwarin gwiwa a yunkurinta na daukar James Tarkowski daga Burnley a bazarar nan. Saura wata 17 kwangilar dan wasan na Ingila mai shekara 28 ta kare kuma har yanzu bai ce zai tsawaita zamansa a Clarets ba, duk da yake a baya sun yi watsi da tayin Foxes da West Ham. (Mirror)

Arsenal za ta yi gogayya da Barcelona a yunkurin daukar dan wasan Manchester Citymai shekara21 dan kasar Sifaniya Eric Garcia, wanda ke shirin barin kungiyarsa a bazara. (Mundo Deportivo via Express)

Everton tana faatawa da Parma domin daukar dan wasanBayern Munich Joshua Zirkzee, mai shekara 19. Ana htunanin cewa Everton ta nemi karbar aron dan wasan na Netherlands tare da zabin sayensa a kan £8.9m. (Sky Germany via Sport Witness)