Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Dzeko, Lingard, Alli, Draxler, Mustafi, Veron da Gray

Edin Dzeko

Asalin hoton, EPA

Edin Dzeko na shirin barin Roma sakamakon rashin jituwar da ke tsakanin dan wasan na Bosnia mai shekara 34 da kocin kungiyar Paulo Fonseca. (Goal)

Ana sa ran tsohon dan wasan na Manchester City zai koma wata daga cikin kungiyoyin da ke buga gasar Firimiya ta Ingila a yayin da yake shirin nade tabarmarsa daga Roma, kuma wasu rahotanni sun ce Everton da West Ham na sonsa. (Gazzetta Dello Sport via Mail)

Kocin West Ham David Moyes shi ma yana son daukar dan wasanManchester United Jesse Lingard bayan rahotanni sun ambato kocin Red Devils Ole Gunnar Solskjaer ya amince dan wasan mai shekara 28 ya tafi wata kungiyar a matsayin aro (Evening Standard)

Sai dai West Hamza ta fuskanci gogayya kan Lingard, wanda aka alakanta da yunkurin tafiya Aston Villa ko Sheffield United. (Express)

Manchester United na aiki tukuru domin ganin ta kayar da kungiyoyin Turai da dama, cikinsu har da Manchester City, Barcelona da Juventus, a fafutukar daukar dan wasan Brazil Gabriel Veron mai shekara 18 daga Palmeiras. (Sport via Star)

Kocin Paris St-Germain Mauricio Pochettino yana son sake hadewa da dan wasanTottenham da Ingila Delle Alli. Sau uku ana kin amicewa da tayin da kungiyar ta yi na daukar dan wasan mai shekara 24, amma Pochettino ya samu goyon bayan kungiyar wajen ci gaba da neman daukar Alli. (The Athletic, subscription required)

A baganre guda, rahotanni sun ce PSG na shirin musayar dan wasan Jamus Julian Draxler, mai shekara 27, da dan wasan Arsenal dan kasar Faransa mai shekara 21 Matteo Guendouzi. (L'Equipe via Mirror)

Udinese na tattaunawa da Wolves domin karbar aron dan wasan Italiya Patrick Cutrone, mai shekara 23. An juya wa dan wasan baya a Molineux tun bayan isar Willian Jose, mai shekara 29 dagaReal Sociedad. (Express & Star)

Kazalika Parma na sha'awar Cutrone, wanda a baya ya yi zaman aro a Fiorentina. (Corriere dello Sport).

Liverpool na dab da kulla yarjejeniyar £1m kan dan wasan Derby County mai shekara 16 Kaide Gordon. Rahitanni na cewa Manchester United da Tottenhamsu ma suna son matashin dan wasan na Ingila.(Liverpool Echo)

Shkodran Mustafi, mai shekara 28, yana tattaunawa da Arsenal a kan kawo karshen kwangilarsa da wuri. Ana rade radin cewa dan kasar Jamus din zai tafi Lazio kuma wasu kungiyoyi na kasarsa su ma suna sonsa. (Football.London)

Monaco da Benfica sun bi sahun kungiyoyin da ke neman dan wasan Leicester City Demarai Gray, mai shekara 24. Kazalika Crystal Palacena son tsohon dan wasan da ke buga tamaula a rukunin Under-21 a Ingila. (Guardian)