Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Odegaard, Lingard, Gilmour, Mbappe, Alaba da Modric

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta kulla yarjejeniyar karbar aron dan wasan tsakiya na kasar Norway Martin Odegaard, mai shekara 22, daga Real Madrid. (Mail)
Kazalika Arsenal ta amince ta biya £1.8m a matsayin kudin aron Odegaard sai dai yarjejeniyar ta ba kungiyar zabin sayen dan wasan. (Times - subscription required)
KocinManchester United Ole Gunnar Solskjaer zai bar dan wasan Ingila Jesse Lingard, mai shekara 28, ya tafi wata kungiyar a matsayin aro a watan Janairun nan sai dai hukumar gudanarwar Old Trafford ce za ta yanke hukuncin karshe kan hakan.(ESPN)
Real Madrid za ta mayar da hankali wajen daukar dan wasan Borussia Dortmund mai shekara 20 dan kasar Norway Erling Braut Haaland, wanda Chelsea da Manchester Unitedsuka so dauka bayan dan wasan Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 22, ya ce ba shi da niyyar barin Paris St-Germain. (Express)
Dan wasanManchester Citydan kasar SifaniyaEric Garcia, mai shekara 20, da takwaransa naLiverpool dan kasar Netherlands Georginio Wijnaldum, mai shekara 30 su ne 'yan kwallon da Barcelonata mayar da hankali domin daukarsu yayin da kwangilarsu ke shirin karewa a bazara. Hakan na faruwa ne bayan kocin Barca Ronald Koeman ya amince cewa yanzu kungiyar ba ta da halin daukar 'yan kwallo. (Mirror)
Newcastle United na shirin tabbatar da nadin Graeme Jones a matsayin koci domin ya taimaka wa manajan kungiyar Steve Bruce, wanda ya amince da nadin. (Telegraph - subscription required)
Babu tabbas game da makomar dan wasan Turkiyya Cenk Tosun a Everton a yayin da aka ki sanya dan wasan mai shekara 29 a cikin tawagar da za ta fafata da Sheffield Wednesday a gasar cin Kofin FA ranar Lahadi. (Liverpool Echo)
Dan kasar Scotland Billy Gilmour, mai shekara 19, zai iya barin Chelsea domin tafiya aro a wannan wata duk da yake ya soma yin nasara a gasar cin Kofin FA a karawar da kungiyarsa ta doke Luton Town, a cewar koci Frank Lampard. (Mail)
Daraktan Real Madrid Emilio Butragueno ya nuna alamar cewa dan wasan Croatia Luka Modric mai shekara 35 zai sabunta kwangilarsa a kungiyar. (Marca - in Spanish)
Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya bukaci hukumar gudanarwar kungiyar da kada ta yi watsi da damar daukar dan wasan Bayern Munich dan kasar Austria David Alaba, mai shekara 28, idan aka bude kasuwar musayar 'yan kwallo a bazara. (Don Balon - in Spanish)
Dan wasanManchester Uniteddan kasar Netherlands Donny van de Beek, mai shekara 23, yana son ci gaba da hakurin zama a Old Trafford duk da yake ba a ba shi dama sosai tun da aka saye si a kan £40m a bazara. (Times - subscription required)
Fenerbahce ta bukaci magoya bayanta su taimaka wajen tara mata kudi bayan ta dauki tsohon dan wasan Jamus Mesut Ozil, mai shekara 32, daga Arsenal. (Mirror)










