Thomas Tuchel: Chelsea ta nada tsohon kocin PSG bayan korar Frank Lampard

Thomas Tuchel

Asalin hoton, Getty Images

Chelsea ta nada tsohon kocin Paris St-Germain Thomas Tuchel a matsayin sabon kocinta inda ya sanya hannu kan yarjejeniyar watanni 18

Tuchel, mai shekara 47, ya lashe kofin League biyu, da kofin ƙalubale na Faransa da a shekaru biyu da rabi da ya yi a PSG.

Chelsea ta kori Frank Lampard bayan watanni 18 yana jan ragamar kulub din.

Tuchel ya kasance koci na 11 da mai Chelsea attajirin Rasha Roman Abramovich ya naɗa tun da ya fanshi kulub ɗin a 2003.

Shi zai jagoranci wasan Chelsea a Stamford Bridge a ranar Laraba da za ta yi da Wolves a gasar Premier.

Ƙungiyoyin da Tuchel ya horar

FC Augsburg II 2007-2008

Mainz 05 2009-2014

Borussia Dortmund 2015-2017

Paris Saint-Germain 2018-2020

Ya fara fito da kansa a 2009 lokacin da ya maye gurbin Jurgen Kloop a Mainz a gasar Bundesliga.

Shekara shida tsakanin ya kara maye gurbin Kloop a Borussia Dortmund a 2015.

Aikin da Tuchel ya yi ne a Dortmund ya sa aka san shi da kokarin da yake a fagen horar da kwallon kafa kuma matashi da ta kai Paris St Germain ta bashi aiki a 2018.

Salon Tuchel a tamaula

Kocin ya yi amfani da salon 4-3-3 a Dortmund da kuma PSG, idan ta kura masa yakan koma salon 3-5-2 ko kuma 5-3-2.

Kawo yanzu Tuchel idonsa ya bude a salon horar da kwallon kafa, har da gasar zakarun Turai da bait aba lashewa ba.

Duk kungiyar da ta dauke shi ya zama wajibi ta yi hakuri ta kuma bashi lokacin da zai samar da sakamakon da ake bukata.