Dalilin da ya sa Manchester United ta fitar da Liverpool daga FA Cup

Liverpool da Manchester United

Asalin hoton, @LFC

Ranar Lahadi Liverpool ta yi ban kwana da FA Cup na bana, bayan da Manchester United ta doke ta da ci 3-2 a wasan zagaye na hudu a karawar da suka yi a Old Trafford.

Karo kuma na 10 kenan da United ke fitar da Liverpool daga FA Cup a fafatawa 15 da suka yi, inda suka yi canjaras hudu, Liverpool ta yi nasara a karawa hudu.

Tun kan karawar Liverpool ta yi nasara a wasa daya ne daga 15 baya da ta ziyarci Old Trafford a dukkan karawa, inda aka doke ta sau 10 da canjaras hudu.

Ko a wasa takwas baya da ta buga a Old Trafford, Liverpool ta sha kashi a karawa hudu da canjaras hudu.

Kuma Manchester United na kokari a gida a FA Cup din, inda ta yi na nasara a wasa takwas baya a kofin - a kakar 1908 zuwa 1912 shi ne ta ci karawa tara a gida da ke tarihi a FA Cup.

Wannan ne karon farko da Liverpool ta yi rashin nasara a wasa biyu a jere tun bayan Maris din 2020.

Liverpool ita ce ta farko mai rike da kofin Premier League a tarihi da aka yi waje da ita a FA Cup tun zagaye na hudu a karon farko, tun bayan wanda Manchester City a kakar 2014-15.

Wannan kuma shi ne wasa na 50 da aka doke Jurgen Klopp tun zuwansa Liverpool cikin watan Oktoban 2015.

Klopp ya ja ragamar Liverpool wasa 295 ya kuma yi nasara a karawa 175 da yin canjaras sau 70.

Liverpool tana da FA Cup bakwai jumulla, sai dai rabonta da ta kofin tun kakar 2005/06.

Yadda Manchester ta ci Liverpool a bugun tazara

Asalin hoton, @ManUtd

Bayanan hoto, Yadda Manchester ta ci Liverpool a bugun tazara

Arsenal ce kan gaba a lashe kofin mai 14, sai Manchester United 12 da Chelsea da Tottenham da kowacce ke da takwas-takwas.

Liverpool ta koma ta hudu a teburin Premier League da maki 34, bayan buga wasa 19, inda Manchester United ce ta daya mai maki 40.

Manchester City mai kwantan wasa ita ce ta biyu da maki 38 sai Leicester City ta uku mai maki iri daya da na kungiyar Etihad.

Wasa biyar da Liverpool za ta buga nan gaba:

Alhamis 28 ga watan Janairu Premier League

Tottenham da Liverpool

Lahadi 31 ga watan Janairu Premier League

West Ham da Liverpool

Laraba 3 ga watan Fabrairu Premier League

Liverpool da Brighton

Lahadi 7 ga watan Fabrairu Premier League

Liverpool da Man City

Asabar 13 ga watan Fabrairu Premier League

Leicester da Liverpool