Frank Lampard: Chelsea ta kori kocinta bayan aikin wata 18

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Alistair Magowan & Simon Stone
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport
Chelsea ta kori kocinta Frank Lampard bayan ya kwashe watanni 18 yana horas da kungiyar.
Tsohon dan wasan tsakiyar na Chelsea, mai shekara 42, zai bar kungiyar da ke matsayi na tara a teburin gasar Premier bayan a makon jiya ta sha kashi a hannun Leicester City.
Wasa daya kacal Lampard ya ci a cikin wasanni biyar da ya buga a baya.
Wasansa na karshe shi ne wanda ya buga da kungiyar Luton a zagaye na hudu na gasar FA ya kuma yi nasara da ci 3-1.
An nada Lampard ya ja ragamar kungiyar na tsawon shekara uku, lokacin da ya maye gurbin Maurizio Sarri a Stamford Bridge a watan Yuli 2019.
A shekararsa ta farko, kungiyar ta kare a matsayi na hudu a gasar Premier, ta kuma je wasan karshe na gasar FA. Amma yanzu kungiyar na fama da rashin nasara a wasanni takwas da ta buga a baya a gasar, kamar yadda suka yi fama a wasanni 23 baya.
A sanarwar da Chelsea ta fitar ta ce,: "Wannan shawara ce mai matrukar wahala da muka yanke, kuam ba shawara ce da mai kungiyar da kwamitin gudanarwarta suka yanke cikin sauki ba.
"Muna godiya ga Frank bisa nasarorin da ya samu a lokacin jagorancin kungiyar. Sai dai, sakamakon da muke samu da kuma kokarin da kungiyar ke yi ba ta kai yadda muke so ba, abin da ya sa kungiyar take tsakiyar teburi kuma babu alamar samun ci gaba.
"Raba gari da gwarzo irin Frank ba abu ne mai dadi ba, amma bayan dogon nazari da tattaunawa an yanke shawarar a kawo sauyi domin bai wa kungiyar damar samun ci gaba da taka rawar da ta dace da samun sakamako mai kyau a kakar wasanni."
Mai kungiyar Roman Abramovich ya ce za a bar mutum-mutumin Lampard saboda yana da muhimmanci ga kungiyar duk da cewa an sallame shi daga aiki.
"Wannan shawara ce mai matukar wuya da aka yanke, ba dan komai ba saboda ina da kyakkywar alaka da Frank kuma ina mutun ta shi," in ji Abromavic.











