Ozil ya ƙara gaba zai fi masa mutunci - Mikel Arteta

AFP

Asalin hoton, AFP

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce kofa a buɗe take ga Mesut Ozil ya bar Kungiyar a wannan watan, bayan rike dan wasan Jamus din tare da kin sanya shi cikin jerin yan wasansa na wannan kakar.

Duk da cewa ya fi kowa yawan daukar kuɗi a ƙungiyar, amma wasa daya kawai ya buga mata na 1-0 da ta yi nasara kan West Ham a ranar 7 ga watan Maris.

Dan shekara 32 ɗin na da sauran wata shida a ƙungiyar a kwantaraginsa, kuma yana da damar tattaunawa da wasu ƙungiyoyin domin komawa kyauta bayan ƙarewar kwantiraginsa a kaka mai zuwa.

Hakan dai zai kawo ƙarshen zamansa na shekara takwas da ya kwashe a Landan a makwanni masu zuwa, yayin da wasu rahotanni daga Turkiyya ke cewa ya fara tattaunawa da kungiyar Fenebache.

"Za mu tattauna domin sanin wane mataki ne zai fi masa kyau a rayuwarsa ta gaba, da shi da kuma wakilinsa, domin ganin mene ne zai fi yi wa kowa daidai," kamar yadda Arteta ya faɗa a ranar Alhamis.

"In mun cimma wani abu a wannan wata zai fi yi wa kowa daɗi, zai yi wa Ozil dadi a rayuwarsa ta gaba, kuma zai fi yi wa Arsenal daɗi".Dan kwallon wanda baya cikin 'yan wasa 25 da ke buga wa Arsenal Premier League da Europa League a bana, ya koma Emirates da taka leda a matakin mafi tsada a kungiyar kan fam miliyan 42.4 a shekarar 2013.Rabonda ya buga wa Arsenal wasa tun ranar 7 ga watan Maris.Kocin Arsenal ya tabbatar da cewar Ozil na yin atisaye da sauran 'yan wasa, amma an bashi hutu bisa wani batun da ya shafe shi a baya.