Ƙalubalen da ke gaban Real Madrid cikin watan Janairu

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid za ta buga gasa uku cikin watan Janairun 2021 da suka hada da La Liga da Spanish Super Cup da kuma Copa del Rey.
Real wadda take ta biyu a teburin L Liga ta shiga shekarar 2021 da kafar dama, bayan da ta doke Celta Vigo 2-0 a gasar Spaniya ranar 2 ga watan Janairu a filin wasa na Alfredo Di Stefano.
A watan na Janairu za ta fafata a karawa uku a La Liga, da daya a Spanish Super Cup wanda ta lashe a bara a Saudiyya da kuma fafatawa a Copa del Rey.
Ranar Asabar, Real za ta ziyarci Osasuna domin buga gasar La Liga karawar mako na 18.
Bayan wasan ne Madrid za ta kara a Spanish Super Cup da Athletic Bilbao ranar 14 ga watan Janairu.
Daga nan ne kuma kungiyar za ta fafata a Copa del Rey zagayen kungiyoyi 16 da suka rage a gasar, amma ba a bayyace wadda za ta fuskanci Real ba kawo yanzu.
Ranar 23 ga watan Janairu, Deportivo Alaves za ta karbi bakuncin Madrid a wasan mako na 19 a Gasar La Liga.
Daga nan kungiyar da Zidane ke jan ragama za ta karɓi baƙuncin Levante a gasar La Liga ranar 31 ga watan Janairun.











