Watakila Ronaldo ya lashe takalmin zinare a gasar Serie A ta bana

Ronaldo ya rike golden boot

Asalin hoton, Ronaldo IG

Farkon kowace shekara da ake shiga kan zama gangara ce wajen lashe gasar kwallon ƙafa ta kasashe musammam a nahiyar Turai don fitar da zakara.

Cristiano Ronaldo bai ba ta lokaci ba wajen shiga shekara ta 2021 da kafar dama, inda ya fara da cin ƙwallo biyu a gasar Serie A ta Italiya, bayan doke Udinese 4-1 ranar Lahadi.

Wannan ce kaka ta uku da Ronaldo ke buga gasar Serie A, wadda ya lashe kofi biyu a jere, amma bai zama kan gaba ba a cin kwallaye a wasanni.

A kakar 2018/19, Fabio Quagliarella na Sampdoria shi ne ya lashe takalmin zinare a Italiya, wanda ya ci kwallo 26, shi kuwa kyaftin din tawagar Portugal, Ronaldo na hudu ya karkare da kwallo 21.

A kakar da ta wuce Ciro Immobile na Lazio shi ne ya zama zakara, bayan da ya ci ƙwallo 36 a gasar ta Serie A, yayin da Ronaldo wanda ya zura kwallo 31 a raga ya yin a biyu.

A kakar bana kuwa Ronaldo ya daura damara lashe takalmin zinare a gasar ta Italiya da ake kiran kyautar da sunan Capocannoniere, kuma tuni yana da 14 a raga kawo yanzu.

Dan wasan yana gaba da Romelu Lukaku da Ciro Immobile da kuma Zlatan Ibrahimovic wajen yawa zura kwallaye a raga a gasar Serie A ta bana.

Ronaldo na shirin karbar takalmin zinare na biyar a fagen zazzaga kwallaye a raga, bayan nasara daya a Premier League da lashe uku a La Liga ta Spaniya.