Barcelona ta bayar da aron Alena ga Getafe

Alena

Asalin hoton, Getty Images

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta bai wa Getafe aron Carles Alena da zai buga mata wasannin aro zuwa karshen kakar tamaula ta bana.

Cikin kunshin yarjejeniyar, Getafe ce za ta biya albashin dan kwallon a zaman da zai yi a kungiyar.

Alena mai wasa daga tsakiya ya buga wa Barcelona wasa 43 ya kuma ci kwallo uku.

A kakar bana kuwa ta 2020/21 ya yi wasa biyar har da biyu a La Liga da karawa daya a Champions League.

Alena wanda ya fara tamaula a matashin dan wasa a La Masia ya fara buga wa babbar kungiyar wasa a Copa del Rey a kakar 2016/17.

Ya zama dan kwallon babbar kungiyar Barcelona a kakar 2018/19, bayan da ya ke taka leda tsakanin matasan kungiyar da kuma Babbar Barcelona.

A Janairun 2020 aka bayar da Alena aro ga Real Betis wadda ya buga wa wasa 19 da cin kwallo daya tal.

Kawo yanzu dan kwallon wanda aka haifa a Cataluanya zai buga wa Getafe wasannin aro zuwa karshen kakar nan.