Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Messi, Ozil, Kean, Son, Traore

.

Asalin hoton, Getty Images

Dan takarar shugabancin Barcelona Agusti Benesito ya ce ba ya tunanin Lionel Messi zai sabunta yarjejeniyarsa a kungiyar, wadda za ta kare a watan Yuni mai zuwa. (Goal)

Manchester ta yi amannar cewa ita ce a kan gaba a layin sayen Messi mai shekara 33 idan dan kasar Argentina din ya bar Barca. (Telegraph)

Sai dai Barca na tunanin sayen wata kungiyar kwallon kafa a gasar Major League Soccer ta Amurka domin taimakawa wurin lallaba Messi ya ci gaba da zama bayan ya ce yana son ya taka leda a Amurka a karshen sana'arsa. (AS)

Dan wasan Arsenal mai shekara 32 Mesut Ozil ya kulla yarjejeniyar shekara uku da rabi da kungiyar Fenerbahce ta Turkiyya. (DHA)

Nan gaba kadan Ozil zai san matsayinsa, a cewar wakilinsa, amma abin da tsohon dan kwallon Jamus din ya fi so shi ne ya ci gaba da zama a Arsenal har zuwa karshen kakar bana lokacin da kwantaraginsa zai kare. (ESPN).

Tottenham na da kwarin gwiwar cewa dan wasan gabanta na Koriya ta Kudu Son Heung-min mai shekara 28 zai saka hannu kan sabuwar yarjejeniya da za ta zaunar da shi a kulob din har gaban 2023, lokacin da kwantaraginsa zai kare. (Telegraph)

West Ham da Wolves na rige-rigen sayen dan wasan Ajax kuma dan kasar Burkina Faso mai shekara 19, Lassina Traore. (De Telgraaf)

Everton na tsammanin PSG za ta nemi sayen dan wasanta Moise Kean dan kasar Italiya, wanda yanzu haka yake wasa aro a birnin Paris din, amma Everton ba ta cikin wata gaggawa wurin yanke hukunci kan rayuwar dan wasan. (Liverpool Echo)