Liverpool na fama da masu tsaron baya da ke jinya a kakar bana

Asalin hoton, Getty Images
Ranar Asabar za a ci gaba da wasannin Premier League karawar mako na tara, inda Liverpool za ta karbi bakuncin Leicester City ranar Lahadi.
Liverpool wadda za ta buga karawar a Anfield tana ta uku a kan teburin Premier League da maki 17, Leicester kuwa ita ce ke jan ragama da maki 18.
To sai dai kuma 'yan wasa hudu masu tsaron bayan Liverpool na jinya, wanda hakan zai iya kawo mata koma baya a kokarin da take na kare kofinta.
Haka kuma Mohammed Salah ya kamu da cutar korona a lokacin da ya je Masar domin buga mata tamaula a karawar shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka.
Shi kuwa Kyaftin din Liverpool, Jordan Henderson ba zai buga wa tawagar kwallon kafa ta Ingila gasar Nations League da za ta yi da Iceland ba.
Sai dai batun da yafi dagawa Liverpool hankali shi ne raunin da mai tsaron baya Virgil van Dijk da Joe Gomez da za su yi jinya zuwa karshen kakar bana.
Shi kuwa Trent Alexander-Arnold da kuma Andy Robertson ba su yi wa tawagar Ingila wasa ba, sakamakon jinya.
Van Dijk ya yi rauni ne a lokacin da Liverpool ta kara da Everton ranar 17 ga watan Oktoba a wasan da suka tashi 2-2 a gasar Premier League, wanda Jordan Pickfordya yi masa keta.
Shi kuwa Gomez ya yi rauni ne a lokacin da yake atisaye a tawagar kwallon kafa ta Ingila, zai kuma yi jinya zuwa karshen kakar bana ta tamaula.
Alexander-Arnold na jinya abin da ya sa bai yi wa tawagar Ingila wasa ba, Kyaftin din Scotland, Robertson shi ma yana jinya.
Mai buga wa Liverpool wasan tsakiya, Fabinho na jinya, bai buga wa tawagar Brazil tamaula ba, kuma bai yi Liverpool karawa uku ba.
'Yan bayan Liverpool da kwazon da suka yi:
Kwazon da masu tsaron bayan Liverpool suka yi a gasar Premier League ta 2019/20.
A kakar bana kuwa ta 2020/21 a wasa daya ne kwallo bai shiga ragar Liverpool ba, yayin da aka zura mata kwallo 16 - Leeds da West Brom sune aka fi zura musu kwallo 17 kowace.
A kakar bara a irin wannan lokacin kuwa kwallo shida ne ya shiga ragar Liverpool, kuma wasa biyu ta buga da ba a ci taba, bayan mako takwas a gasar ta Premier League.
A shekarar nan Aston Villa ta ci Liverpool 7-2 ranar 4 ga watan Oktoba a gasar ta Premier League.
Kawo yanzu Joel Matip ne kadai mai tsaron baya daga tsakiya keda lafiya a Liverpool kawo yanzu, shi ma yana da matsalar rauni, inda wasa uku kacal ya buga a bana.
An kuma tabbatar cewar dan wasan tawagar Kamaru ba zai iya buga wasa uku a mako daya ba, domin za a samu matsala.
Kwazon masu tsaron bayan Liverpool a 2020/21:
Wasannin mako na tara da za a buga a gasar Premier League:
Asabar 22 ga watan Nuwamba
- Newcastle United da Chelsea
- Aston Villa da Brighton & Hove Albion
- Tottenham da Manchester City
- Manchester United da West Bromwich Albion
Ranar Lahadi 22 ga watan Nuwamba
- Fulham da Everton
- Sheffield United da West Ham United
- Leeds United da Arsenal
- Liverpool da Leicester City
Ranar Litinin 23 ga watan Nuwamba
- Burnley da Crystal Palace
- Wolverhampton Wanderers da Southampton











