Edouard Mendy: Chelsea ta sayi golan Senegal daga Rennes

Mendy has made 34 appearances for Rennes since joining the club from Reims in August 2019

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mendy is Frank Lampard's eighth summer signing

Chelsea ta sayi gola Edouard Mendy daga Rennes a yarjejeniyar shekara biyar.

Dan wasan na Senegal, mai shekara 28, ya buga wasanni 25 a Rennes bayan ya je kungiyar daga Reims a 2019.

An kammala duba lafiyarsa ranar Talata, yayin da kocin Chelsea Frank Lampard ya ce yana so a rika gasa tsakaninsa da Kepa Arrizabalaga, wanda aka saya a kan £71m.

"Ina farin cikin zuwa Chelsea," in ji Mendy. "Na dade ina son zuwa wannan kungiyar."

Kepa ya yi kuskure a kwallo ta biyu da Liverpool ta zura wa Chelase a gasar Firmiya ranar Lahadi, kuma Lampard ya ce hakan "kuskure ne karara."

A kakar wasan da ta wuce an ajiye dan wasan na Sufaniya bayan ya rika tafka kura kurai.

Cikinsu har da a wasan karshe na gasar cin Kofin FA, lokacin da aka maye gurbin golan mai shekara 25 da gola na biyu Willy Caballero, mai shekara 38.

A kakar wasan da ta wuce, Mendy ya hana a zura kwallo a ragar Rennes a wasanni tara a cikin wasanni 24 na Ligue 1 da ya buga, idan aka kwatanta da kwallo takwas da Kepa ya hana a zura a ragar Chelsea a wasanni 33 da ya buga na gasar Firimiya.

Mendy ya tare kwallo kashi 76.3 cikin kashi 100 da aka harba masa kuma ya bari an ci kwallo daya a cikin kowadanne minti 114.

A nasa bangaren, Kepa ya tare kwallo kashi 53.5 cikin 100, sannan ya bari an ci kwallo daya cikin kowadanne minti 63.

Mendy, wanda ya buga wasannin kasashen duniya guda takwas, ya zama dan kwallo na takwas da Frank Lampard ya saya tun da aka bude kasuwar saye da musayar 'yan kwallon kafa a bana.