Edouard Mendy na daf da kulla yarjejeniya da Chelsea

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ta auna koshin lafiyar mai tsaron ragar Rennes, Edouard Mendy daga baya zai rattaba hannu kan yarjejeniya a kungiyar.
Frank Lampard na bukatar golan tawagar Senegal mai shekara 28 domin ya hada shi gogayya da Kepa Aririzabalaga wanda ta saya mafi tsada a tarihi kan fam miliyan 71.
Mai tsaron raga Kepa shi ne ya yi kuskuren da Liverpool ta ci Chelsea kwallo na biyu a karawar Premier League da suka fafata ranar Lahadi.
Kepa dan kasar Spaniya ya yi zaman benci a kakar bara, bayan kurakuren da ya dunga yi a wasanni.
Ciki har da karawar karshe a FA Cup, wanda daga baya aka cire shi mai shekara 25 aka saka Willy Caballero a wasan mai shekara 38.
Bayan da Liverpool ta doke Chelsea 2-0 ranar Lahadi, Lampard ya ce Caballero ne zai tsare ragar kungiyar a wasan Caraboa Cup da Barnsley a Stamford Bridge ranar Laraba.
A bara Mendy ya hana kwallo ya shiga ragarsa sau tara daga wasa 24 da ya buga wa Rennes gasar Ligue 1, idan ka kwatanta da Kepa wanda wasa takwas kwallo bai shiga ragarsa ba a fafatawa 33 a Premier.
An fahimce cewar Mendy ba wai zai maye gurbin Kepa bane, illa dai da dazar Caballero wanda zai cika shekara 39, da zarar ya bar tamaula an samu madadinsa cikin sauki kuma matashi.











