Thiago Silva: Ɗan wasan Brazil ya tafi Chelsea daga PSG

Thiago Silva

Asalin hoton, Chelsea FC

Bayanan hoto, Silva ya jagoranci PSG a matsayin kyaftin

Kungiyar Chelsea ta sanar da kulla yarjejeniya da dan kwallon Brazil, Thiago Silva a kwangilar shekara daya domin murza leda a Stamford Bridge.

Silva wanda dan wasan baya ne a Paris Saint- German, ya kasance daya daga cikin zaratan 'yan wasan da Chelsea ta siya domin shiryawa kakar wasa mai zuwa.

Zuwan shi Chelsea na zuwa ne bayan da kungiyar ta sayi Ben Chilwell daga Leicester a ranar Laraba da kuma da Malang Sarr daga Nice.

Thiago ya ce: "Na ji dadin kasancewa cikin tawagar Frank Lampard domin fafatawa a kakar wasa mai zuwa".

Dan kwallon mai shekaru 35 ya samu nasarori sosai a lokacin da yake murza leda a PSG.