Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Magalhaes, Havertz, Dybala, Costa

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal na da kwarin gwiwar kammala sayen dan wasan Lille Gabriel Magalhaes a kan £22m. Everton da Napoli suna zawarcin dan kwallon na Brazil mai shekara 22. (ESPN)
Chelsea za ta kammala kulla yarjejeniya da dan wasan Bayer Leverkusen Kai Havertz, mai shekara 21, nan da kwana 10 masu zuwa. Dan wasan na Jamus yana son kwangilar shekara biyar a Stamford Bridge. (Bild, via Express)
Watakila Juventus ta saka dan wasan gaba Paulo Dybala, mai shekara 26, a cikin musayar da za ta karbo dan wasan Manchester United Paul Pogba. Dan kasar Argentine Dybala yana da sauran shekara biyu a Juventus. (Tuttosport - in Italian)
A gefe guda, Man Utd na sanya ido dan dan wasan Juventus mai shekara 29 dan kasar Brazil Douglas Costa. (Sky Sports)
Watford ta yi watsi da tayin Everton na daukar dan wasan tsakiya Abdoulaye Doucoure. Watford tana son £25m kan dan wasan na Faransa mai shekara 27. (Standard)
Lazio na duba yiwuwar dauko dan wasan West Ham da Brazil Felipe Anderson, mai shekara 27, bayan David Silva ya ki amsa tayinta. (Star)
Chelsea za ta tattauna kan kwangila da dan wasan tsakiya Conor Gallagher a yayin da Newcastle da Crystal Palace ke zawarcinsa. Dan wasan mai shekara 22 ya kwashe kakar wasan da ta wuce yana zaman aro a Swansea. (Mail)
Burnley tana tattaunawa domin dauko dan wasan Angers Baptiste Santamaria. Aston Villa ta so dauko dan kasar Faransa, mai shekara 25, a kan £12m a shekarar da ta wuce. (RMC Sport, via Daily Mail)
Brighton ta ce kyaftin dinta Lewis Dunk, mai shekara 28, da mai tsaron baya Ben White, mai shekara 22, za su ci gaba da zama a kungiyar. An yi ta rade radin cewa Dunk zai tafi Chelsea yayin da Leeds ke zawarcin White. (Talksport)
Aston Villa tana da kwarin gwiwar cewa za ta ci gaba da rike Douglas Luiz, mai shekara 22. Ana rade radin cewa dan wasan na Brazil yana son komawa Manchester City. (Express and Star)
Sheffield United na duba yiwuwar karbo aron golan Manchester United dan kasar Ingila Dean Henderson, mai shekara 23, duk da amincewa ta ba da kudi don dauko dan wasan Bournemouth Aaron Ramsdale, mai shekara 22. (ESPN)
Norwich na son dauko dan wasan West Ham Jordan Hugill, mai shekara 28. (Mail)
Southampton tana tattaunawa da Schalke don dauko dan wasan Amurka mai shekara 21 Weston McKennie a kan £20m. (Sky Sports)











