Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Messi, Aubameyang, Magalhaes, Griezmann, Alcantara, Dybala

lionel messi and antoine griezmann

Asalin hoton, Getty Images

Lionel Messi ya gaya wa Barcelona cewa yana son barin kungiyar nan take, kuma Manchester City ce kan gaba cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan Argentina mai shekara 33. (Esporte Interativo, via Mirror)

Arsenal ta amince da sharuda kan sabuwar kwangilar kyaftin dinta Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 31, kuma tana dab da sayen dan wasan Brazil Gabriel Magalhaes, mai shekara 22, daga Lille. (Telegraph)

Barcelona za ta sayar da dan wasan Faransa Antoine Griezmann, mai shekara 29, shekara guda kacal bayan ta saye shi daga Atletico Madrid a kan £107m. (Sport via Express)

Dan wasan Bayern Munich Thiago Alcantara ya amince da kwangilar shekara hudu da Liverpool, kuma kungiyar da ke buga gasar Bundesliga tana son a biya ta fiye da £30m kan dan wasan na Sufaniya mai shekara 29. (RMC Sport, via Mirror)

Juventus ta shirya sayar da dan wasanta mai shekara 26 Paulo Dybala kuma Manchester United da Tottenham na zawarcin dan wasan gaban na Argentina. (Gazetta Dello Sport - in Italian)

Kazalika Juventus na son dauko dan wasan Arsenal dan kasar Faransa Alexandre Lacazette ko kuma dan wasanWolvesdan kasar Mexico Raul Jimenez, dukansu masu shekara 29. (Sky Sports)

Inter Milan na zawarcin dan wasanManchester United Chris Smalling, mai shekara 30, kuma watakila ta biya £20m kan dan wasan na Ingila. (Metro)

Leicester na fuskantar gogayya daga Paris St-Germain kan dan wasan Atalanta da Belgium Timothy Castagne, mai shekara 24. (Calciomercato via Leicestershire Mercury)

Leeds United na son dauko dan wasan Jamus da Freiburg Robin Koch, mai shekara 24, a yayin da take-kasa-tana-dabo kan kulla yarjejeniya da dan wasan Brighton Ben White, mai shekara 22. (Telegraph - subscription required)

Dan wasan Manchester United da Faransa da ke buga rukunin 'yan kasa da shekara 19 Aliou Traore, yana dab da tafiya zaman aro Caen. (Goal)