John Mikel Obi: Stoke City na dab da ɗauko ɗan wasan na Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Stoke City na dab da sayen tsohon ɗan wasan Chelsea John Mikel Obi kan yarjejeniyar shekara ɗaya.
Tsohon kaftin din na Najeriya mai shekara 33, ba ya da wata ƙungiya a yanzu bayan ya baro Trabzonspor ta Turkiya a watan Maris.
Tun a farkon mako ya shaida wa BBC cewa zai dawo taka leda a Ingila.
Mikel ya buga wa Chelsea wasanni 249 a Premier League a shekaru 11 kafin ya bar Stamford Bridge a 2017.
Ya lashe kofin zakarun Turai na Champions League da Europa League, da kofin Premier League guda biyu da kofin FA uku da kuma League Cup a Chelsea.
Bayan ya bar Stamford Bridge ya koma kulub din China na Tianjin TEDA kuma ya taka leda a Middlesbrough a 2019.
Mikel ya buga wa Najeriya wasa 89, ya wakilci ƙasar a gasar cin kofin duniya biyu tare da taimaka wa Super Eagles lashe kofin Afirka kafin ya sanar da yin ritaya daga buga wa ƙasarsa wasa.







