Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Gabriel, Havertz, Wilshere, Thiago, Sancho, Doucoure, Rodrigo

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal na dab da kammala dauko Gabriel Magalhaes. An gama duba lafiyar dan wasan na Brazil mai shekara 22 wanda Lille ta amince ta sayar da shi a kan £27m. Arsenal ta ba shi kwangilar shekara biyar, sai dai har yanzu Napoli ba ta karaya ba kan kokarin dauko shi. (Times, subscription required)
Idan Napoli ta gaza dauko Gabriel, za ta ita yunkurin dauko dan wasan Arsenal dan kasar Jamus Shkodran Mustafi, mai shekara 28. (Daily Star)
Manchester United tana son dauko dan wasan na Brazil, sai dai dole ta zage damtse idan tana so ta sayo shi. (Daily Star)
Chelsea na dab da dauko Kai Havertz bayan ta sake tattaunawa da Bayer Leverkusen a kan farashin dan wasan na Jamus mai shekara 21. (Guardian)
Kazalika Chelsea ta yi nisa a tattaunawarta da kyaftin na Paris St-Germain Thiago Silva, a yayin da dan wasan mai shekara 35 dan kasar Brazil yake shirin barin PSG bayan wasan karshe na Kofin Zakarun Turai da za su fafata da Bayern Munich ranar Lahadi. (The Athletic, subscription required)
GolanLille Mike Maignan, mai shekara 25, yana cikin 'yan wasan da Stamford Bridge ke son karbowa. (Le10 Sport via Star)
Manchester City ta amince ta kulla yarjejeniya da Napoli kan dan wasanSenegal Kalidou Koulibaly, mai shekara 29. (Sports Illustrated)
Abokan wasan Jadon Sancho a Borussia Dortmund sun yi amannar cewa dan wasan na Ingila mai shekara 20, wanda ake sa ran zai tafi Manchester United, zai ci gaba da zama a kungiyar da ke buga gasar Bundesliga zuwa karin shekara daya bayan ya yi atisaye na gabanin soma kakar wasa. (Telegraph, subscription required)
Kocin Juventus Andrea Pirlo ya cire Gonzalo Higuain, mai shekara 32, da dan wasan tsakiya Sami Khedira, mai shekara 33, daga tawagarsa. (Mirror)
Everton na son bai wa dan wasan Faransa mai shekara 27 Abdoulaye Doucoure £120,000 duk mako a kokarin dauko shi daga Watford. (Football Insider)
Leeds United na shirin dauko dan wasanValencia da Sufaniya Rodrigo, mai shekara 29. (Mail)











