Europa: Wasan share fagen Europa ya zama sili daya kwale

kocin Tottenham Jose Mourinho

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Koci Jose Mourinho na Tottenham ya kammala gasar Premier 2019/20 a matsayi na shida a gasar

Tottenham za ta je Bulgaria domin barje gumi da Lokomotiv Plovdiv a wasa rukuni na biyu na wasan share fagen shiga gasar Europa.

Duka wasannin rukuni na biyu za a buga su fale daya ne kamar yadda aka yi a gasar zakarun Turai da ta Europa, za a buga su ne duka a ranar 17 ga wasan Satumba kuma ba tare da 'yan kallo ba.

Ko da an tashi canjaras a wasannin za a tafi Karin lokaci in ta kure ma akai ga bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Sauran wasannin da za a buga Shamrock Rovers ta jamhuriyar Ireland za ta fafata da AC Milan yayin da Rangers za ta buga nata wasan da lincon Red.

Ga dai cikakken jadwalin wasannin da za a fafata:

  • Inter Escaldes v Dundlak
  • Linfield v Floriana
  • Connah's Quay Nomads v Dinamo Tbilisi
  • B36 Torshavn v The New Saints
  • Coleraine vs Motherwell
  • Viking v Aberdeen
  • Bala Town v Standard Liege
  • Lokomotiv Plovdiv v Tottenham Hotspurs
  • Lincoln Red Imps v Rangers
  • Shamrock Rovers v AC Milan