Messi ya fi so ya auri Man City a kan PSG, Sadio Mane zai tafi Barcelona

Mahaifin Lionel Messi ya shaida wa Paris St-Germain cewa dan wasan Barcelona da Argentina, mai shekara 33, ya fi son murza leda a Manchester City. (L'Equipe - in French)
Messi ya kira kocin Manchester City Pep Guardiola ranar Talatar da ta wuce - kafin ya shaida wa Barcelona cewa yana son barin kulob din - inda ya gaya masa cewa 'Ina son lashe gasar Ballon d'Or guda biyu na gaba, kuma zan cika wannan buri ne kawai idan ina tare da kai'. (Marca)
Shugaban Barcelona Josep Maria Bartomeu ya ki amincewa ya gana da Messi domin su daddale kan barinsa kungiyar inda ya dage cewa dole dan wasan ya ba da £624m idan yana so ya tafi. (El Periodico - in Spanish)
Chelsea na son dauko golan AC Milan da Italiya Gianluigi Donnarumma, mai shekara 21. (Football Insider)
Barcelona na son dauko dan wasan Liverpool da Netherlands Georginio Wijnaldum, mai shekara 29. (Goal)
Everton ta amince da wata yarjejeniya da dan wasan Real Madrid James Rodriguez, mai shekara 29, bayan dan wasan na Colombia ya kwashe kakar wasa biyu da suka wuce yana zaman aro a Bayern Munich.(beIN via Sun)
Za a duba lafiyar dan wasan Jamhuriyar Ireland Matt Doherty, mai shekara 28, a Tottenham ranar Asabar bayan sun amince su biya Wolves €12m kan dan wasan. (Football London)
Dan wasan Senegal Sadio Mane, mai shekara 28, ya shirya barin Liverpool inda zai tafi Barcelona don haduwa da tsohon kocin Southampton Ronald Koeman. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Dan wasan Freiburg da Jamus Robin Koch, mai shekara 22, ya amince da yarjejeniyar tafiya Leeds United. (Football Insider)
Manchester United na dab da kammala sayen matasan 'yan wasan Sufaniya Marc Jurado, mai shekara 16, da Alvaro Fernandez, mai shekara 17, wadanda za su bar tawagar matasan 'yan wasan Barcelona da Real Madrid. (Sky Sports)











