Messi ya tuntubi Guardiola kafin ya rubuta wa Barcelona takardar saki

Asalin hoton, Getty Images
Shahararren dan wasan Argentina Lionel Messi, mai shekara 33, ya tuntubi kocin Manchester City Pep Guardiola a makon jiya inda ya gaya masa cewa yana son barin Barcelona, a cewar jaridar Times - subscription required.
A shirye Manchester City take ta bayar da 'yan wasan Sufaniya Eric Garcia, mai shekara 19, da Angelino, mai shekara 23, a cikin yarjejeniyar dauko Messi. (Manchester Evening News)
Kazalika Manchester City ta shirya bai wa Barcelona £89.5m tare da 'yan wasan da suka hada da Garcia, Bernardo Silva, da Gabriel Jesus domin karbo Messi. (Sport - in Spanish)
Real Madrid za ta nemi a biya ta fiye da euro 20m kan dan wasan Sufaniya mai shekara 23, Sergio Reguilon, wanda ya ja hankalin Manchester United, Tottenham, Juventus da kuma Inter Milan a yayin da yake zaman aro a Sevilla. (Marca)
Chelsea ta kusa kammala hada £90m don sayo dan wasan Jamus mai shekara 21 Kai Havertz daga Bayer Leverkusen. (Guardian)
Tsohon dan wasan Sweden Zlatan Ibrahimovic, mai shekara 38, ya amince da sabuwar kwangilar shekara daya a AC Milan inda aka yi amannar cewa zai karbi kusan £6m. (Sky Sports Italia - in Italian)
Dan wasan Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 35, ya kawar da jita-jitar da ake yi a kansa ta barin Juventus inda ya ce yana shirin buga wasanni na kakarsa ta uku a kungiyar. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Dan wasan Faransa Antoine Griezmann ya yanke hukuncin barin Barcelona kafin sabon koci Ronald Koeman ya lallabi dan wasan mai shekara 29 ya ci gaba da zama a kungiyar. (RMC Sport via Metro)
Isar dan wasan Jamhuriyar Ireland Matt Doherty Tottenham daga Wolves za ta bayar da dama ga dan wasan Ivory Coast Serge Aurier ya bar kungiyar. (Standard)
Manchester United ta nemi dauko dan wasan Brescia Sandro Tonali, mai shekara 20, wanda ake gani a matsayin daya daga cikin gwarazan matasan 'yan wasan Italiya. (Corriere dello Sport via Metro)











