Enrique zai koma kocin Spain bayan mutuwar 'yarsa

Luis Enrique

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto, Luis Enrique

Luis Enrique, zai cigaba da horas da kungiyar kwallon kafar kasar Sifaniya, bayan wata biyar kenan da kocin ya ajiye aikinsa.

Enrique ya ajiye aiki a watan Yuni bayan ya yi wata biyar yana jan ragamar kungiyar, sai dai a watan Agusta ya sanar da mutuwar diyarsa 'yar shekara tara mai suna Xana, sakamakon ciwon daji.

Tsohon kocin Barcelona mai shekara 49 an maye gurbinsa da mataimakinsa, Robert Moreno.

Moreno na rike da ragamar kungiyar kwallon kafar Sifaniya lokacin da kasar ta doke Romania da ci 5-0.

Hakan ya sanya Spain ta kammala wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Euro 2020 ba tare da an doke ta ba.

Moreno, wanda shi ma ya yi aiki karkashin Enrique a Roma, Celta Vigo da Barcelona, ya ce zai ajiye mukamin a duk lokacin da Enrique din ya bukaci dawowa.

A wani taron manema labarai ranar Talata, Shugaban Hukumar Kwallon kafa ta Sifaniya, Luis Rubiales ya ce: "Kowa ya sani cewa idan Luis Enrique yana son dawowa to kofa a bude take.

"Luis Enrique zai ci gaba da rike ragamar kungiyar har zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a shekara ta 2022."

An nada Enrique a matsayin mai horas da 'yan kwallon kasar bayan ficewar Sifaniya daga gasar cin Kofin Duniya na 2018 a zagaye na 16.

Dan kasar Sifaniya din ya dawo gida ne saboda wasu dalilai kafin wasan da kasar ta samu nasarar cin 2-0 a Malta, lamarin da ya sanya aka maye gurbinsa da Moreno na wucin gadi.

Bayan wata uku ne Enrique ya sanar da matakinsa na ajiye aiki.