Super Eagles: Najeriya ta casa Lesotho har gida

Asalin hoton, @NGSuperEagles
Super Eagles ta Najeriya ta samu galaba a kan Lesotho a wasan neman shiga gasar cin Kofin Kasashen Afirka da za a yi a shekarar 2021.
Dan wasan Lesotho Masoabi Nkoto ne ya zira kwallon farko a ragar Najeriya cikin minti na 11 da fara taka-leda.
Dan wasan Najeriya Alex Iwobi ya farke ta a minti na 22, yayin da Samuel Chukwueze ya zira ta biyu a minti na 38.

Asalin hoton, @NGSuperEagles
Sai kuma Victor Osimhen, wanda ya ci ta uku da ta hudu a minti na 75 da 85.
Amma ba a tashi ba sai da Chidozie Awaziem na Lesotho ya cilla wa Najeriya kwallo ta biyu a zare a minti na 90.
Super Eagles ce kan gaba a rukuni na 12 da makinta shida, yayin da Benin take biye mata da maki uku, sai kuma Lesotho da Sierra Leon masu maki daya kowaccensu.
Sau uku kenan Najeriya tana doke kasar a irin wannan wasan, bayan da ta casa ta a shekarar 2006 da ci 1-0 ta hannun Yakubu Aiyegbeni.
Sai a 2007 da ci 2-0 ta kafar Stephen Ayodele Makinwa da Ikechukwu Uche da kuma wannan shekarar ta 2019 da ta samu galaba a kan ta da ci 4-2.
Najeriya za ta karbi bakuncin kasar ta Lesotho a karshen shekarar 2020.











