Firimiyar Najeriya: Kano Pillars ta sha kashi a hannun Lobi Stars

Asalin hoton, @pillarsfc
Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta sha kashi har gida a hannun Lobi Stars da ci 1-0 a gasar Firimiyar Najeriya.
Dan wasan Lobi Stars Douglas Achiv ne ya zira kwallon cikin minti na 62.
Karo na biyu kenan da Pillars take tashi ba tare da samun nasara ba - ta yi canjaras daya sannan kuma an doke ta a guda daya.
Yanzu haka dai kungiyar ta Pillars na mataki na 17 a teburi da maki daya kacal.
Ita kuwa Lobi Stars tana mataki na biyar da maki shida.
Sauran sakamakon wasannin da aka buga:
Abia Warriors 1 - 1 Sunshine Stars
Delta Force FC 4 - 1 Jigawa Golden Stars
Enugu Rangers 0 - 1 MFM FC
Enyimba 3 - 1 Akwa United
Heartland Owerri 1 - 1 Akwa Starlets
Ifeanyi Ubah United 1 - 0 Rivers United FC
Katsina United 1 - 0 Nasarawa United
Plateau United 2 - 1 Wikki Tourist
Warri Wolves FC 2 - 0 Adamawa United











